Daya daga cikin fitattun masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa a shiyyar Daura, kuma daya daga cikin ‘ya’ayan Masarautar Kasar Daura, Sarkin Sudan na Daura, Alhaji Rabe Yusuf, ya bayyana cewar ba shi da hannu ko goyon baya a takaddamar da ake yi kan turo wasu a matsayin ‘yantakara a yankin.
Sarkin Sudan na Daura ya bayyana hakan ne a wata zantawa da manema labarai, ciki har da jaridun Katsina Times, a ranar Asabar, inda ya ce batun da ke yawo kan batun wasu sun fiddo ‘yantakara a yankin ba tare da amincewar jama’a ba, bai da nasaba da shi.
“Maganar cewa an fiddo wani ya yi takara ba tare da yardar jama’a ba, ni ba da yawuna ba. Batun cewar an fiddo wasu su tsaya takara, ni ma ji na yi kamar yadda kowa ya ji,” in ji shi.
Da yake tsokaci kan rade-radin da ke yawo kan batun turowa ko fiddo Yusuf Buhari don yin Takara, ya ce shi ma bai da tabbacin hakan, in ma an yi ba da yawunsa ba.
“Batun Yusuf Buhari, ni ba da yawuna ba babu ruwana. Abin da kuka ji, ni ma haka na ji,” ya kara da cewa.
Game da maganar tsayawa takarar Sanata da aka ce shugaban Majalissar Dokoki, Nasiru Yahaya Daura na sha’awar fitowa kuwa, ya bayyana cewar ya taba zantawa da shi kan batun, inda ya ce masa mutane ne ke matsa masa ya fito takara.
“Na tambaye shi ko akwai wanda ya saka shi, sai ya ce a’a. Ya ce jama’a ne ke kiran shi suna bukatar ya tsaya takara, shi kuma ba ya kin bukatar jama’a,” in ji Sarkin Sudan.
A kan hakan, Alhaji Rabe Yusuf ya jaddada cewar tsarin mulkin kasa ya bai wa kowa damar tsayawa takara, don haka bai kamata a takaita hakan ga wani mutum daya ba.
“Ai Siyasa, ra’ayi ne. Ba wanda zai tilasta wa wani ya yi ko kar ya yi. Don haka duk wanda yake da sha’awa, ya je ya nemi goyon bayan jama’a, su ne ke zabe. Kowa na da ‘yancin tsayawa takara,” ya bayyanar, yana mai kari da cewa zai gana da masu ruwa da tsaki domin jaddada wannan matsaya.
Hakazalika, Sarkin Sudan ya nuna damuwarsa kan yadda ake samun takaddama a karamar hukumar Daura, duk da cewa sauran yankunan jihar na cikin kwanciyar hankali.
“Abin da ke ba ni mamaki shi ne, babu matsala a sauran yankuna, amma a Daura ake samun wannan rikici. Me ya same mu? Mun raina na gaba ne ko kuwa?” ya tambaya cikin takaici.
Harwayau, dangane da zargin cewar ko kila yana goyon bayan wasu ‘yantakara, ya musanta hakan, yana mai cewa ba zai taba sabawa doka ba wajen fifita wani ba, ko sa6awa ra’ayin jama’a ko za6insu ba.
“Ba zan taba cewa wani ya fito ko wani ya janye ba. Amma idan jama’a suka nuna suna son wani, to ina tare da su,” in ji shi.
Ya kuma kara da cewar bai dace a ce mutum daya tilo ne zai tsaya takara ba, yana mai cewa bayyana hakan a matsayin abin da bai dace ba kuma ba tsarin dimokuradiyya ba ne.
A karshe, Alhaji Rabe Yusuf ya ce yana rike da mukaminsa na shuagaba masu ruwa da tsaki ne domin hidimtawa al’ummar Daura, ba don wata fa’ida ta kashin kansa ba, yana mai kalubalantar duk wanda ke da hujjar cewa ya taba cin gajiyar mukamin ta hanyar samun wani abu daga masu rike da madafun iko kamar karbar kwangila; alawus; albashi ko makamancin haka daga wani shugaban karamar hukuma ko gwamna to ya fito da ita fili.
Haka kuma ya ce idan akwai masu ganin bai dace ya ci gaba da rike mukamin ba, to za su iya bin hanyoyin da aka dora shi domin a cire shi, yana mai bayyana cewar “Ni a shirye nake akodayaushe in aka ce in sauka daga mukamin in sauka.” ya karkare.


