Saturday, June 13, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiBuni Ya Rage Kudin Hayar Taraktoci Da Kashi 50 Cikin 100

Buni Ya Rage Kudin Hayar Taraktoci Da Kashi 50 Cikin 100

Daga Sani Gazas Chinade Damaturu

Manoma a fadin jihar Yobe sun sami babban ci gaba yayin da gwamna Mai Mala Buni ya amince da rage kashi 50 cikin 100 na kudin hayar tarakta motocin noma wanda ya rage kudin daga naira 100,000 zuwa naira 50,000.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Dr Mohammed Goje sakataren riko na gwamnatin jihar, yadda ya bayyana wannan shiri a matsayin wani shiri na rage nauyin da ke kan manoma, fadada damar yin noma ta injinan, da kuma inganta yawan amfanin gona a fadin jihar.

A cewarsa, rage kudin hayar tarakta zai bai wa qarin manoma damar noma manyan gonaki, kara yawan amfanin gona, a lokacin noma na yanzu.

“Rage kashi 50 cikin 100 na kudin hayar tarakta zai bai wa manoma da yawa damar noma mafi girma a gonaki, kara yawan amfanin gona, a lokacin noman da ake ciki,” in ji Dakta Goje.

Ya jaddada cewa ana sa ran wannan matakin zai rage yawan kudin noma sosai, habaka samar da abinci, karfafa tsaron abinci, da kuma inganta walwalar tattalin arzikin al’ummomin jihar da akasarin su manoma ne.

Dr Goje ya jaddada cewa gwamnatin gwamna Buni ta ci gaba da sanya noma a sahun gaba a cikin ajandar ci gabanta ta hanyar zuba jari mai dorewa a tarakta, injunan noma, ingantattun iri, taki, tallafin noman rani, da sauran shirye-shiryen da suka dace da manoma wadanda aka tsara don karfafa al’ummomin karkara da kuma karfafa ci gaban tattalin arziki.

Sakataren gwamnatin jihar na rikon kwarya (SSG) ya kara bayyana cewa sanya ayyukan tarakta su zama masu araha zai karfafa shiga cikin ayyukan noma, habaka yawan aiki, da kuma tallafawa kokarin jihar na samar da wadatar gona da kan iya haifar da samun abinci a wadace.

Ya sake nanata alkawarin gwamnatin Buni na aiwatar da manufofi da shirye-shirye wadanda ke habaka ci gaban noma, kirkirar damar samun aikin yi, inganta rayuwa, da kuma tabbatar da ci gaban tattalin arziki mai dorewa ga al’ummar jihar Yobe.

Ana ganin rage kudin hayar tarakta a matsayin wani mataki mai karfafa gwiwa da gwamna Buni ya dauka wajen tallafawa manoma, kara yawan samar da abinci, da kuma gina Jihar Yobe mai wadatar abinci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments