Daga Imrana Abdullahi
Ministan da ke kula da ayyukan ma’aikatar Gidaje ta tarayyar Najeriya Injiniya Dokta Muttaqha Rabe Darma, ya tabbatarwa da duniya cewa shi ya na nan tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu dari bisa dari kuma ya na masa biyayya baki daya.
Muttaqha Rabe Darma ya ce kamar yadda ya yi shekaru a ƙalla Goma Sha hudu baya komai sai dai idan dan aikin bayar da shawara ya samu a wani wuri kawai ya dan je ya yi aikin don haka tun da a yanzu ya samu aiki da Bola Tinubu ya bashi na muƙamin minista hakika ya na tare da shi kuma ya na masa biyayya matukar biyayya.
“Ko da dana na ciki na zai zo gaba na ya na zagi a kan batun Bola Ahmed Tinubu hakika Ni da shi mun raba gari”.
“Hakika duk wanda aka ce shi ne minista na kaza koda na kwasar kashi ne mutum sai ya ji dadi kuma nima na ji dadin kwarai lamarin dadin ya sosa Mani zuciya, kuma damar da shugaban kasa ya bani ba zan ba shi kunya ba kuma ba zan ba mutanen Najeriya kunya ba,kuma mutanen jihar Katsina da suka amince cewar zan iya rikon muƙamin ministan da aka ba Ni ba zan ba su kunya ba.
Kuma, ” Ko kafin a ba Ni muƙamin ministan ma da akwai wadansu mutane da yawa da suka rika ce Mani ga mukami nan ya taho kai har ma wasu na cewa in yi sadaka domin ga mukami nan ya taho amma duk lamarin bai dauke Ni ya Dada Ni da kasa ba, Ni dai ina iyakar yi na wajen tafiyar da harkokin rayuwar yau da kullum saboda na san duk abin da ke naka a rayuwa ko yaya kake sai ya zo gare ka”.
“Ina son shaidawa jama’a cewa mun yi ta kai ruwa rana Ni da wani abokina tun kafin a ba Ni muƙamin ministan da nake a kai a yanzu, kuma ina shaidawa jama’a cewa sai da aka yi Mani intabiyu sau uku kafina a bani kuma shugaban kasa ne da kansa yake yi Mani don ya ga cewa ko zan iya yin aikin da ya ba ni,kuma sau Uku aka yi Mani wannan intabiyu, amma sauran ba san yadda aka yi masu na su ba tun da ban inda aka yi masu na su ba,Ni dai an kira Ni an karbi takarduna kuma an Mani tambayoyi na bayar da amsa kuma bayan yan wasu watanni aka sake kira na amma wannan ban ga shugaban kasa ba na dai ga wasu mukarraban Gwamnati manya aka sake yi Mani tambaya don haka a wannan lokacin ne wani daga cikin manyan ma’aikatan yake gaya Mani cewa tun da kaga an sake kiranka na biyu to, lallai kai ne
Kuma Daya daga cikin wadanda ke taimako na a wannan lamarin shi ne Alhaji Ibrahim Kabir Masari, domin yi wa shugaban kasa aikin da yake son ayi masa.
“kuma Ni duk wanda ya san Ni ya san bayan ma an yi Mani wannan intabiyu kashi kashi sai da aka yi watanni hudu zuwa kusan ma biyar har na shiga ina ta yin takarar kujerar majalisar dattawa kuma a ranar da aka sanar da suna na ma sai da na je yawon Kamfe har kananan hukumomi Uku na kuma ga ji can da yamma ina wani wuri kwance sai wani abokina ya kira Ni da wata lambar musamman da ba kowa nake ba ita ba ina bacci na farka da na dauka sai yake gaya Mani cewa in ta Shi in duba tashar talabijin ta kasa NTA, Ni na ma dauka wani ne ya mutu kawai sai na tambaye shi lafiya sai ya ce ai an ba Ni minista hakika abin ya yi Mani dadi kwarai da gaske don haka ba za mu bayar da kunya ba cikin yardar Allah sai mun kawo ci gaba a wannan ma’aikata don mun ma rigaya mun fara”.
“Hakika aikin ni a yanzu Ban dauke shi da wani bambanci da aikin da na yi na koyarwa a jami’ar Bayero ba ko aikin injiniyan hada motoci da na yi a kamfanin da na yi aikin ba ko na aikin sayar da motoci a kamfanin BMW ba ko aikin da na yi a hukumar PTDF ba ko aikin daraktan gudanar da bincike a gidan Gwamnatin Jihar Katsina ba ko wani bambanci da darakta SEPA na Jihar Katsina ba ko kuma aikin Kwamishina da na yi sau biyu ba a jihar Katsina ba.
“Idan an baka aiki aka dora maka nauyi abubuwa biyu ko Uku ne ke a gabanka na farko ladabi da biyayya ga wanda ya baka aikin don haka ne nake goyon bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu baki daya ina yi masa biyayya”.
” Sai da na yi shekaru Goma sha hudu ina zaune ba na aikin komai sai idan dan aikin bayar da shawara ya samu irin na masana kawai ayi shi idan an samu a cinye abin da aka samu har sai ayi shekaru biyu ko uku ba komai, kai har Janaretici na sayar wadanda nake da su domin a ci gaba da harkar rayuwa domin dai a ganka a babban mutum amma a ciki ba a san abin da ke ciki ba tun da Bola Tinubu ya ba Ni minista hakika ina yi masa ladabi da biyayya ga shugaban kasa don haka wannan babban muƙamin da aka ba Ni na minista a kasar nan ko dana zai zo gaba na ya zagi Tinubu lallai mun raba gari da shi.


