Daga Sani Gazas Chinade Damaturu
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da naɗin Alhaji Yerima Ibn Mahmud a matsayin sabon Sarkin Ngazargamu Mai hedikwatar Mulki a garin Gaidam cikin jihar Yobe.
Sanarwar naxin na qunshe a cikin takardar yin hakan da Muƙaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar, Dakta Mohammed Goje, ya fitar a ranar Juma’a aka rabawa manema labarai.
Shi sabon Sarkin Ibn Mahmud zai gaji marigayi Sarkin Ngazargamu, Alhaji Tijjani Ibn Saleh Geidam, wanda ya rasu a ranar Talata a ƙasar Masar bayan fama da doguwar rashin lafiya wadda aka yi jana’izarsa a ranar Juma’a a Damaturu fadar jihar.
Kafin naxin sabon Sarkin Ibn Mahmud ya riƙe muƙamin Kwamishinan bunƙasa kiwo na Jihar Yobe, ya kuma kasance Turakin Ngazargamu na tsawon shekaru 16.
Haka nan a baya sabon sarkin ya taɓa riƙe muƙamai daban-daban a gwamnati, ciki har da zama ɗan majalisar dokokin Jihar Yobe da kuma kwamishina a jihar a lokuta mabambanta tsakanin shekarar 2007 da 2026 da a yanzu aka nasa shi sabon Sarkin Ngazargamu.
Kamar yadda sanarwar ke cewa , sabon Sarkin ya bayar da gagarumar gudummawa wajen tafiyar da gwamnati, tsara manufofi da kuma bunƙasa tattalin arziki da zamantakewa a tsawon shekarun da ya yi yana hidimar jama’a kafin yanzu.
A cikin jawabin sa yayin da ya ke taya sabon Sarkin da al’ummar masarautar murna, gwamna Buni ya buƙace shi da ya yi amfani da ƙwarewarsa wajen ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba a masarautarsa ta Ngazargamu.
“Ina taya sabon Sarkin Ngazargamu da ɗaukacin al’ummar masarautar murnar wannan naɗi da aka masa,” in ji Gwamna Buni.
“Don haka ina kira ga Mai Martaba da ya yi amfani da gogewarsa wajen haɗa kan jama’a, inganta zaman lafiya da zaman tare cikin aminci, tare da ƙarfafa bunƙasar tattalin arziki a masarautar, Jihar Yobe da Nijeriya baki ɗaya,” in ji Buni.
Ya kuma yi kira ga al’ummar masarautar da su bai wa sabon sarkin cikakken goyon baya domin samun nasarar gudanar da ayyukansa cikin nasara.
“Ina kira ga al’ummar masarautar da su bai wa sabon Sarkin cikakken goyon baya domin ya sauke nauyin da ke kansa cikin jajircewa, nagarta da inganci, domin amfanin jama’a da kuma ci gaba da wanzar da zaman lafiya, haɗin kai da wadata a masarautar.”in ji Buni.
Gwamna Buni ya yi addu’ar Allah Ya ba sabon Sarkin hikima, lafiya da kuma mulki mai cike da zaman lafiya da albarka da kan iya kai shi ga nasara.


