Daga Imrana Abdullahi
Kungiyar Northern Comrades Movement da ke tarayyar Najeriya, (NCMN) karkashin jagorancin Malam Jabir Ibrahim Yaro da ake kira da Mallam Jabir, sun koka a game da irin yadda ake kashe al’umma a yankin Arewacin kasar.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a wajen wani gagarumin taron manema labarai da suka kira a Kaduna inda suka tabbatar da korafinsu game da dimbin matsalolin da suka dabaibaye kasar wanda a ciki kuma wanda ya fi ƙamari shi ne kisan al’umma ba gaira ba dalili da ake yi a cikin birane da yankunan karkarar yankunan Najeriya baki daya.
Kungiyar sun karantawa manema labarai wata takardar da suka fitar mai dauke da sa hannunsa suna masu kokawa da matsalar da ake fama da ita na kashe mutane da kuma hana manoma yin sana’arsu ta Noma har sai sun biya wadansu makudan kudi kuma duk da hakan ma ba a yi masu abin da ya dace wato ba a barinsu su yi Noma haka wajen cire amfanin Gonarsu ba a barinsu nan ma sai sun biya.
Sun kuma koka a kan irin yadda ake kashe jami’an tsaro a arewacin Najeriya
“Ga duk wanda ya san mu a tsawon shekaru Goma da suka gabata an san irin yadda kungiyar ke kokarin kare hakki martaba da mutuncin mutane ta hanyar yi wa Gwamnati magana ta yi wa jama’a abin da yakamata.
Kungiyar ta kuma ce ta na wayarwa da jama’a kai game da abubuwan da suka shafi harkokin siyasa domin su san cewa siyasa da ba batun kabilanci ba ne domin duk abubuwan da ake gani a harkar siyasa ya shafi daukacin rayuwar al’umma baki daya kuma kungiyar na tallafawa marasa karfi a lokaci zuwa lokaci”, inji shugaba Jabir.
Sai ta kara jaddada dalilan da suka sa kungiyar ta kira taron manema labarai a garin Kaduna inda suka ce hakan ya faru ne sakamakon irin yadda matsalar kashe- kashe ke faruwa a Najeriya domin lamarin ya wuce yankin arewa ta Yamma, ko arewa ta Gabas ko arewa ta tsakiya ya karade kasa ne baki daya.
“Don haka ne a matsayin mu na matasa da muke ganin muna da sauran lokacin da za mu zauna a kasar nan bai kamata mu yi shuru ba domin lamari ne da zai cinye mu baki daya saboda haka a halin yanzu har ma wadanda suka kasance jami’an tsaron da ke aikin kare lafiya da dukiyar jama’a ma ba su tsira ba. Din haka ne muke ganin wadanda Allah ya dora alhakin magance wannan matsalar sun kasa yin abin da Yakamata na magance matsalar duk da ana sace jama’a tare da yi wa Mata Fyade duk an kasa magance matsalar don haka muke cewa ba mu yarda ba a matsayin mu na yan kasa dole mu yi wa shugabnni magana su tashi tsaye a magance matsalar da take a cikin jama’ar kasa.
“Muna kira a gare ku, shugabanni ku fito a gyara kasa mun gaji da wannan matsalar saboda a batun gaskiya an san inda za a je a ga masu yin wannan kashe kashen jama’ar kasa an san inda za a gamsu.
Masana da dama har da mu kan mu duk mun zauna mun tattauna matsalar nan, sannan kuma masana da dama a kan harkar tsaro duk sun yi bincike sun bayyana irin yadda farkon matsalar take da yadda za a samu magance ta amma duk abin da aka yi an ki yin aiki da shi ballantana a samar da maganin matsalar baki daya.
” Mun babban taro a kan shugabanci da harkar tsaro kuma mun gabatar da duk abubuwan da muka tattauna ga wadanda ke da alhakin hakan amma har yanzu ba komai ba a samu wani ci gaban da jama’a za su ce sam Barka ba don haka mun gaji da wannan matsalar sai kawai zai ana raba wa mutane Shinkafar da muma za mu iya Noma wa a nan kasar
“A matsayin mu na matasa kuma na kungiya muke cewa wannan matsalar tsaron fa a kai karshenta domin a yanzu a Najeriya Akuya ta fi ka tabbacin rayuwa”.
An yin amfani da wannan damar mu yi wa yan uwa matasa magana a kan harkar siyasa, lallai matasa su daina siyasa saboda addini ko Kabilanci a kuma daina siyasa saboda wani abu da za a samu, muna son a rika yin siyasa don kawai mutum ya cancanta kuma matsa su daina bari ana amfani da su wajen bangar siyasa da sauran wadansu abubuwan da ba su kamata a samu matashi a ciki ba.


