Daga Sani Gazas Chinade Damaturu
Dakarun rundunar hadin gwiwa ta arewa maso gabas, Operation Haxin Kai (OPHK) sun kama wasu mutane hudu da ake zargin suna hada kai da kungiyoyin Boko Haram da ISWAP, a wasu hare-haren da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri a jihohin Yobe da Borno.
Har ila yau, rundunar ta ce sojojinta sun yi tare-tare da kama wasu mutane 20 da ake zargin ‘yan uwan mayaqan qungiyar Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad (Boko Haram) ne, wadanda suka tsere daga maboyarsu a Jihar Borno sakamakon matsin lambar hare-haren da sojoji ke kai musu.
Mukaddashin Jami’in Yada labarai na rundunar Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar talata.
Ya ce dakarun Bataliya ta 159 da ke karkashin Sector 2 sun gudanar da samame tare da bincike a garin Geidam na Jihar Yobe a ranar 3 ga Agusta, bayan samun sahihan bayanan sirri, inda suka kama mutane biyu da ake zargin masu hada kai da ‘yan ta’adda ne.
A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin suna samar wa mayaqan Boko Haram miyagun kwayoyi da sauran kayan tallafi domin saukaka ayyukansu.
Kayayyakin da aka kwato daga hannunsu sun hada da tabar wiwi da ake zargi, wayoyin hannu iri-iri, na’urorin adana wuta (power banks), almakashi, wukake, fitilun hannu, abubuwan kunna wuta (lighters), sigari, kwayoyin Pregabalin, maganin tari na Piscof, katin shaidar dan kasa (NIN), katin zaxe na dindindin (PVC), katunan ATM da kuma kudi Naira 14,530.
Goni ya kara da cewa, a wani samame daban da aka gudanar da misalin karfe 3:30 na rana a wannan rana, dakarun Sector 3 Garrison tare da hadin gwiwar Bataliya ta 242 Reconnaissance sun kama wasu mutum biyu da ake zargin masu samar wa ISWAP kayan tallafi ne a garin Monguno na Jihar Borno.
Ya ce yayin binciken farko, waÉ—anda ake zargin sun amsa cewa suna kai wa mayakan ISWAP kayan abinci da sauran kayayyaki a kauyen Kwatan Dowoshi da ke karamar hukumar Kukawa.
Kayayyakin da aka kwato sun hada da kwalaye 11 da ledoji 192 na biskit iri-iri, kwalin madarar Peak guda daya, mudu 10 na sukari, sabulai Viva guda tara, fitilun kai guda shida, buhu biyu da kuma kunshi 16 na garin rogo (garri) da aka zuba a leda, fakiti uku na abubuwan kunna wuta, wayoyin Tecno masu maballi guda biyu, sharveviyar wuqa guda daya, damarar laya, tasbihi guda hudu, fakiti shida na magungunan gargajiya, kudi naira 6,600 da sauran kayayyaki.
A wani ci gaba kuma, rundunar ta ce dakarun Bataliya ta 222 sun tare, tare da kama wasu mutum 20 da ake zargin ‘yan uwan mayakan Boko Haram ne yayin sintiri a yankin Gezuwa da ke karamar Hukumar Konduga a Jihar ta Borno.
Mutanen sun hada da manyan mata tara, maza biyu, kananan ‘yan mata takwas da karamin yaro namiji guda daya.
A cewar rundunar, mutanen sun shaida wa masu bincike cewa sun tsere daga Gezuwa ne sakamakon hare-haren da sojoji ke kai wa maboyar ‘yan ta’addar.
Rundunar ta ce an mika mutanen ga rundunar leken asirin Soji ta 21 domin tantance su da daukar matakan da suka dace, yayin da aka kuma tare da mika mutane hudun da aka kama da dukkan kayayyakin da aka kwato ga sassan leken asirin soji domin ci gaba da bincike.
Rundunar ta Operation Hadin Kai ta bayyana cewa wadannan nasarori sun nuna irin tasirin dabarun tattara bayanan sirri da rundunar ke amfani da su wajen katse hanyoyin samar wa ‘yan ta’adda kayan tallafi da kuma rushe hanyoyin da suke samun goyon baya.
Rundunar ta kuma yi kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin lokaci domin karfafa yaki da ta’addanci da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin arewa maso gabas.


