Friday, August 28, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiRundunar OPHK Ta Dakile Yunkurin Da 'Yan Ta'adda Suka Yi Na Sace...

Rundunar OPHK Ta Dakile Yunkurin Da ‘Yan Ta’adda Suka Yi Na Sace Dalibai A FGGC Monguno Da Ke Borno

Daga Sani Gazas Chinade Damaturu

Sojojin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan Najeriya (MOPOL), sun yi nasarar dakile yunkurin sace wasu dalibai da ‘yan ta’addar ISWAP suka yi a Kwalejin ‘yan mata ta gwamnatin tarayya (FGGC), Monguno, da misalin karfe 1:30 na dare wayewar garin ranar 19 ga Yuli, 2026.

Gwamnatin Jihar Borno a halin yanzu tana amfani da wannan makaranta ta FGGC a matsayin masaukin baki na wucin gadi ga daliban Kwalejin fasaha ta tarayya da ke, Monguno.

Wannan bayani ya fito ne daga cikin wata sanarwa da mukaddashin jami’in yada labarai na Soja, hedikwatar rundunar hadin kai ta Maiduguri, Kyaftin Mohammed Goni ya sanya wa hannu kuma ya bayar ga manema labarai, inda ya ce ‘yan ta’addar sun sami damar shiga sansanin tare da taimakon wasu waxanda ake zargi da haxin gwiwa a yunkurin sace daliban.

Ganin hakan ke da wuya jami’an tsaro nan da nan suka yi wa ‘yan ta’addan luguden wuta, inda suka dakatar da ci gaba da kai hari da rundunar Sashe na 3 Quick Reaction Force (QRF) nan take.

Saboda karfin fada da karfin dakarun tsaro hakan ya tilastawa ‘yan ta’addan barin aikinsu na kokarin sace daliban suka gudu cikin rudani ba tare da cimma burinsu ba.

Kyaftin Goni ya ce a lokacin fafatawar, sassan kayayyakin makarantar sun lalace amma sojoji tare da jami’an ‘yan sandan Najeriya sun shawo kan yunkurin.

Ya ce bayan aikin, sojoji sun yi nasarar ceto tare da kwashe dukkan dalibai 46 zuwa barikin Kinnasara, Monguno, inda suka sami gwajin lafiya nan take da kuma kulawar da ta dace.

A cewar mukaddashin kakakin rundunar na Soja, an tabbatar da cewa dukkan daliban da aka ceto suna cikin koshin lafiya kuma babu wani dalibi da aka sace.

Majiyar ta qara da cewa wani abin takaici, wasu dalibai sun mutu sakamakon harbin bindiga daga ‘yan ta’addan a lokacin fafatawar.

Ya ce “Operation HADIN KAI tana mika ta’aziyyarta ga iyalan mamatan tare da tabbatar wa jama’a cewa ana daukar dukkan matakan da suka wajaba don kare rayukan mazauna yankin da kuma kare muhimman cibiyoyin gwamnati a fadin yankin arewa maso gabas tare da hadin gwiwa da gwamnatin Jihar Borno.

Ana ci gaba da amfani da lamarin don gano da kuma kama wadanda ake zargi da hadin gwiwa, yayin da sojoji da sauran hukumomin tsaro ke bin diddigin ‘yan ta’addan da suka gudu.

“Operation HADIN KAI ta ci gaba da dagewa kan jajircewarta na ci gaba da matsin lamba ga bangarorin ‘yan ta’adda, hana su ‘yancin daukar mataki, wargaza karfin aikinsu, da kuma tabbatar da cewa cibiyoyin ilimi da sauran muhimman kayayyakin more rayuwa a fadin yankin arewa maso gabas suna cikin aminci da kwanciyar hankali.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments