Friday, August 28, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamnatin Yobe Ta Amince Da Ware Naira Miliyan 460.8 Don Tallafawa Masu...

Gwamnatin Yobe Ta Amince Da Ware Naira Miliyan 460.8 Don Tallafawa Masu Tuyar Kosai, Sauran Kananan Sana’o’i

Daga Sani Gazas Chinade Damaturu

Gwamnatin Jihar Yobe ta amince da ware naira miliyan 460.83 don karfafawa masu kananan kasuwanci mata, ciki har da masu tuyar kosai da sauran kananan sana’o’i a mazabu 178 da ke fadin jihar.

Wannan amincewar wani bangare ne na kudurorin da aka cimma a taron majalisar zartarwa ta Jihar wanda Gwamna Mai Mala Buni ya jagoranta a gidan gwamnati da ke Damaturu.

Da yake yi wa manema labarai jawabi bayan taron, kwamishinan harkokin cikin gida, da al’adu, Alhaji Abdullahi Bego, ya ce matakin da aka dauka an yi shi ne don tallafawa mata da ke gudanar da kananan kasuwanci da sana’o’i ta hanyar samar da muhimman abubuwa don habaka rayuwarsu.

“Majalisar zartarwa ta Jihar ta amince da naira miliyan 460,828,450.00 don sayen wake don rarrabawa ga mata a matsayin tallafin karfafa musu gwiwa kan harkokin sana’o’i da kasuwancin su.

“Za a rarraba musu wake ne tare da man girki, murhu na zamani maras hayaki, kayan girki da kayan kicin, wadanda ma’aikatar samar da arziki, karfafawa da samar da aiki ta riga ta sayo kuma ta adana su.

“Za a raba jimillar buhun wake 1,780 mai nauyin kilogiram 50 ga wadanda za su amfana,” in ji shi.

“A karkashin ma’aikatar samar da arziki da aikin yi, majalisar ta amince da ware naira miliyan 364,475,000.00 don sayen injunan nika nau’in Yamaha GX 390 guda 1,000 don tallafawa ga mutane a fadin jihar,” in ji shi.

Kwamishinan ya kara da cewa majalisar zartarwa ta amince da gudanar da ayyuka da suka kai naira biliyan 73.32 a sassa masu muhimmanci na tattalin arzikin jihar.

A cewarsa, amincewar “sun hada da ware naira biliyan 28.53 don sayan kayan aikin noma don shirin karfafawa manoma gwiwa na jihar na wannan shekara ta 2026, da kuma ware naira biliyan 23.97 don manyan ayyukan hanya guda biyu, da kuma ware kudade don harkokin gidaje, kasuwanni da sauran ayyukan ababen more rayuwa.”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments