Friday, August 28, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeSiyasaJam'iyyar APC,Tinubu Da Uba Sani Ne Za Su Lashe Zabe A 2027...

Jam’iyyar APC,Tinubu Da Uba Sani Ne Za Su Lashe Zabe A 2027 – Musa Bawa Ciki Da Waje

…..Baffa Babba Dan Agundi ya bayar da yakin zamani a Kaduna

Daga Imran a Abdullahi

Sakamakon irin yadda Gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani ke tafiyar da jagoranci domin inganta rayuwar al’umma hakan ya sa ba tare da shakka ko wata tantama ba a shekarar 2027 su za su lashe zabe da gagarumin rinjaye.

Shugaban kungiyar APC Ciki da waje na Jihar Kaduna da ke fafutukar ganin Tinubu da Uba Sani sun sake cin zabe Musa Bawan FCNA ya tabbatarwa da duniya cewa ba tare da wata tantama ba jam’iyyar APC karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani za su lashe zaben cikin sauki.

Sai dai ya ce babban dalilinsa na yin wadannan kalamai shi ne irin yadda Gwamnatin tarayya da Gwamna Uba Sani ke yin aiki dai dai Gwargwadon iko da nufin inganta rayuwar jama’a.

“Babu wasu yan Adawa a halin yanzu da suke iya yin wata hobbasa domin a koda yaushe sai dai ka gansu suna canza jam’iyya daga wannan zuwa waccan kawai abin da ke tabbatar da cewa ba su da tudun dadawa, don haka jam’iyyar APC kawai ita ce mafita”.

Musa Bawa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kaddamar da rabon Yakin zamani da za a ba kungiyoyin da ke yin aiki tare da kungiyar APC Cikin da waje a Jihar Kaduna.

Yakin dai an kawo shi ne daga ofishin Daraktan Janar national productivity Center Abuja, mai kula da Shiyyar arewa maso Yamma, da ta ƙunshi jihohi Bakwai,Dokta Baffa Babba Dan agundi da aka ƙaddamar a Kaduna.

Dokta Baffa Babba Dan Agundi dai ya kawo Takin zamani mai suna Nagari kuma an kaddamar da buhuna dari biyu da za a raba wa wadannan ya’yan kungiyoyi daban daban

Musa Bawa FCNA ya kuma ce wannan rabon kaya ba shi ne karo na farko da ofishin Dokta Baffa Babba Dan Agundi ya kawo aka kuma raba a Karkashin kungiyar APC ciki da waje ba, wannan karo na a ƙalla biyar kenan ana raba wa.

Sai dai a wajen taron an yi bayanin irin yadda za a raba takin inda aka ce a ƙalla akwai mutane 50 daga kowace Marabar dan majalisar dattawa da ke jihar Kaduna a yanki Uku da ake da su da hakan ya kama mutane dari da Hamsin kenan da za a raba wa Takin.

Jama’ar da suka taru a wajen duk sun nuna kin dadinsu da irin kokarin da Dokta Baffa Babba Dan Agundi ke yi na kawo kayan alkairi a jihar Kaduna domin jama’a.

Dokta Baffa Babba Dan Agundi ne da kansa ya halarci wajen kaddamar da rabon Takin zamanin da aka yi a harabar ofishin APC ciki da waje a Kaduna.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments