Saturday, June 13, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeSiyasaJam'iyyar APC A Jihar Yobe Ta Amince Ma Shugaba Tinubu Wa'adi Na...

Jam’iyyar APC A Jihar Yobe Ta Amince Ma Shugaba Tinubu Wa’adi Na Biyu 2027

Daga, Sani Gazas Chinade Damaturu

Taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Yobe sun amince da Shugaba Bola Ahmed Tinubu GCFR a matsayin dan takara daya tilo don tsayawa takara a karo na biyu a Zaben 2027.

An amince da Shugaban a ranar Alhamis a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a Damaturu ta hanyar kudirin da Sanata Ahmad Ibrahim Lawan ya gabatar kuma Kakakin majalisar dokokin Yobe, Hon. Chiroma Buba Mashio ya goyi bayansa, yayin da dukkanjn masu ruwa da tsaki suka amince da shi baki daya.

Gwamna Mai Mala Buni ya yi wa masu ruwa da tsaki jawabi, ya ce a matsayinsa na memba na jam’iyya mai mulki, jihar ta amfana da gwamnatin tsakiya wacce ke karkashin Jagorancin jam’iyyar APC matukar gaske.

“Abin farin ciki ne cewa hadin gwiwarmu da jam’iyyar kasa da gwamnati tun daga shekarar 2015 ya jawo wasu fa’idodi ga jihar, wanda ya saukaka shirinmu na sake ginawa da dawo da martabar jihar da al’ummarta.

“Don haka ina kira ga mutanen jihar nagari da su sake goyon bayan Jam’iyyar All Progressives Congress tare da amincewa da Shugaba Tinubu na wani wa’adi na shugabanci a karo na biyu” in ji Buni.

Ya yaba wa masu ruwa da tsaki kan nuna balaga ta siyasa mai girma wacce zaman lafiya da muradun jihar da al’ummarta suka haifar.

“Kodayake muna iya samun matsayi da ra’ayoyi daban-daban na siyasa, ba mu taba barin tashin hankali ya faru a rayuwarmu ta siyasa ba.” Wannan shaida ce cewa lallai mu ne gidan “Siyasa ba tare da kaucewa ga ra’ayin mu na hadaka ba ko kuma gaba da juna ba,” kamar yadda daya daga cikin shugabannin siyasa masu hazaka, marigayi Alhaji Waziri Ibrahim ya ba da shawara.

Ina so in yi amfani da wannan lokacin don gode wa mutanen jihar nagari saboda juriya da goyon bayan da kuka ba wa gwamnati a koƙarinmu na murmurewa, ba wai kawai don sake gina jihar ba, har ma don saukaka rayuwa ga mutanenmu.

Ga jami’an tsaronmu, gwamnati da mutanen jihar Yobe nagari suna matukar nuna godiya ga jajircewarku wajen yaki da rashin tsaro yayin da wasu daga cikinku sun bada gudummawar su ga jihar Yobe don ta kasance cikin zaman lafiya, yadda sadaukarwar ku ba ta taba zama banza ba domin yanzu muna jin dadin zaman lafiya da muka samu a sakamakonn irin sadaukar da rayukanku da Kuka yi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments