Saturday, April 18, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeSiyasaAPC Ta Karbi Kungiyoyi 293 Na PDP A Jihar Yobe

APC Ta Karbi Kungiyoyi 293 Na PDP A Jihar Yobe

Daga, Sani Gazas Chinade Damaturu

A wani gagarumin sauyi na siyasa a Jihar Yobe, Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi ram da ƙungiyoyi 293 daga Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai adawa a Karamar Hukumar Potiskum.

Ficewar jama’a, wacce ita ce mafi girma a yankin a ‘yan kwanakin nan, ta samu jagorancin Shugaban PDP na Karamar Hukumar Potiskum, Alhaji Audu Hamisu, wanda aka fi sani da “Soja Boy.”

Masu sauya shekar sun fito ne daga ƙungiyoyi da dama na ƙasa, ciki har da Tora-Bora, Texaco, Sokol-Jigawa, Dorawa, Kabul, Kamfala, Old Kwata, Rasha da Big Soja duka a garin Potiskum.

Da yake jawabi yayin da yake karɓar masu sauya shekar a Potiskum, Shugaban APC na Jihar Yobe, Alhaji Muhammad Gadaka, ya bayyana jam’iyyar a matsayin mai haɗaka da kuma maraba, yana mai danganta ƙarfinta da ƙaruwar masu shigowa cikin akullum.

Ya yaba wa manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni, yana mai kira ga sabbin membobin da su bayar da gudummawa sosai ga nasarar jam’iyyar a zabuka masu zuwa.

“Jam’iyyar APC wani dandali ne mai fadi wanda ke ba da damammaki iri ɗaya ga dukkan ‘yan jam’iyya, ba tare da la’akari da asalinsu ba.

“Don haka Ina roƙonku da ku haɗa kai cikin sauri ku yi aiki don nasarar jam’iyyar a zaɓe mai zuwa,” in ji Gadaka.

A cikin jawabinsa, Hamisu ya ce shawarar ficewa daga tsohuwar jam’iyyar su ta PDP ta biyo bayan shawarwari da sake duba ayyukan APC a matakin jiha da tarayya.

Ya ambaci ci gaban tsaro, manufofin tattalin arziki da ci gaban jama’a a matsayin muhimman abubuwan da suka haifar da wannan matakin.

“Bayan yin nazari mai zurfi, mun gamsu cewa makomar siyasarmu tana hannun APC,” in ji shi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments