Saturday, April 18, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeSiyasaSanata Ahmed Lawan Ne Ya Cancanci Zama Angon Jihar Yobe A 2027...

Sanata Ahmed Lawan Ne Ya Cancanci Zama Angon Jihar Yobe A 2027 Inji–Nasiru Mato

Sani Gazas Chinade Daga Damaturu

Shugaban gamayyar kungiyar magoya bayan tsohon shugaban majalisar dattijai na 9 Sanata Ahmed Ibrahim Lawan na jihar Yobe Alhaji Nasiru Mato ya bayyana cewar, in lokacin zabe ya yi a shekarar 2027 babu wanda ya cancanta da tsayawa takarar gwamna a inuwar Jam’iyyar APC mai mulkin kasa da Jihar ta Yobe da ya wuce Sanata Ahmed Ibrahim Lawan.

Alhaji Nasiru Mato ne ya bayyana haka ne a tattaunawar sa da wakilinmu a garin Potiskum dangane da yadda shirye-shiryen gangamin siyasa ya ke gab da fara daukar harami.

Shugaban ya kara da cewar, “duk da cewar da sauran lokaci dangane da gudanar da zabuka to amma duk haka kamar yadda malam bahaushe ne ke cewar da zafi-zafi kan bugi karfe hakan ne ya sa su magoya bayan Ahmed Lawan ke kokarin yin Shiri don fuskantar yakin dake gaban mu.”

“A cewar sa babban abin da ya ja hankalin su don kafa wannan kungiya ta su ta goyon bayan Sanata Ahmed Ibrahim Lawan don tsayawa takarar gwamna a zaben da ke tafe na 2027 wadda kungiyar da suka yiwa lakabi da, daga Buni sai Bade shi ne, don duba cancanta wadda kuwa wannan gwani namu tsohon shugaban majalisar dattawa ta tara Sanata Ahmed Lawan in ka duba ka sa akan faifai ka kuma auna akan sikeli zaka tarar da cewar, ya fi kowane dan takarar da zai fito don neman wannan kujerar gwamna cancanta matukar gaske saboda irin sanin da ya ke da shi akan harkokin mulkin musamman ma mulki irin na dimukuradiyya lura da cewar tun da aka fara dimukuradiyya a wannan lokaci a 1999 ya ke zauren majalisar kasa.”

Ya kara da cewar, a siyasance Ahmed Ibrahim Lawan wakilin al’umma ne na kwarai da ya bautawa siyasa, ya bautawa Jam’iyyar sa ya kuma bautawa al’ummar sa da ma al’ummar kasa baki daya wadda kan haka ne muke ga mutum ne da ya cancanta da shugabantar al’ummar Jihar Yobe in lokacin ya yi.

“Alhaji Nasiru Mato ya kara da cewar suna da yakinin matukar lokaci ya yi na zabe aka zabi Sanata Ahmed Ibrahim a matsayin gwamnan Jihar Yobe zai dora ne akan wurin da gwamna Mai Mala Buni ya tsaya lura da cewar shi mutum ne da ke da kudirin bautawa jama’ar sa.”

Shugaban ya kuma mayar da martani ga wasu mutanen da ke yarfen siyasa ga gwanin na su na cewar wai har ya kare shugabancin majalisar dattawa na kasa babu wasu ayyukan kirki da ya yiwa yankunan Jihar Yobe illa ya tabe ne a mazabar sa ta arewacin Yobe (zone c), ya ce, masu wannan zargi su sani fa cewar a wancan lokacin shi Sanata Lawan yana shugabantar harkokin kasa ne baki daya kana ya na wakiltar al’ummar sa ne na arewacin Jihar Yobe illa in dama ne ta samu tukun zai dora hannun sa akan wasu sassan Jihar ta Yobe wadda kuwa na tabbatar ya gudanar da wasu ayyukan raya kasa a wasu bangarorin da ba cikin mazabar sa ta arewacin Jihar suke ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments