Daga Sani Gazas Chinade Damaturu
Gwamnatin Jihar Yobe ta dage dokar hana fita daga tsakiyar dare domin bai wa mazauna yankin, musamman musulmai, damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin kwanciyar hankali ba tare da wani sharadi ba.
Mai ba da shawara na musamman ga gwamnan kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Dahiru Abdulsalam (Rtd), ya bayyana hakan ga manema labarai bayan wani taron tsaro da mataimakin gwamnan jihar Alhaji Idi Barde Gubana ya jagoranta.
Dahiru Abdulsalam ya ce majalisar tsaron Jihar ta yi la’akari da yanayin watan Ramadan da aka shiga shi ya sa ta ga ya zama wajibi a sassauta dokar don bai wa al’ummar musulmai damar gudanar da ayyukansu na addini cikin kwanciyar hankali ba tare da wani tarnaki ba.
Ya bayyana cewa majalisar ta duba yanayin tsaro a fadin jihar kuma ta yanke shawarar karfafa matakan kariya a duk lokacin azumin Ramadan.
A cewarsa, Ramadan yana da halaye daban-daban na addini, ciki har da wa’azi, tarurrukan karawa juna sani, addu’o’in jama’a, buda baki, da kuma Qiyamul laili wadanda da yawa daga cikinsu suna tsawaita har zuwa tsakar dare kuma suna bukatar kasancewar akwai walwala lura da cewar hukumomin tsaro na sa ido akai.
Ya lura cewa an kira taron tsaro ne domin tantancewa da kuma yin nazari kan yanayin tsaro a fadin jihar da kuma tabbatar da cewa al’ummar Jihar sun yi azumin Ramadan cikin kwanciyar hankali, tare da kare rayukansu da dukiyoyinsu yadda ya kamata.
Mai ba da shawara kan tsaron ya kara da cewa a irin wannan lokacin, wasu masu aikata laifuka na iya kokarin boye kansu don aikata laifukan da ba su dace ba.
Don haka ya yi kira ga mazauna jihar da su ci gaba da tallafawa hukumomin tsaro ta hanyar samar da bayanai masu inganci don ci gaba da zaman lafiya da ake samu a jihar.
Dahiru Abdulsalam ya kuma nuna damuwa kan ayyukan hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a yankin Gulani na karamar hukumar Gulani, yana mai jaddada cewa hukumomin tsaro sun riga sun shawo kan lamarin.


