Ana neman wata baiwar Allah mai suna Hajiya Turai Runka mai kimanin shekaru 80 wadda ta ɓace.

Ta na sanye da hijabi mai ruwan ƙasa da riga mai ruwan shudi (blue). Ta ɓace daga unguwar Bayan Liyafa tun safiyar ranar Laraba 8/4/2026 da misalin ƙarfe 8:00 na safe.

Duk wanda ya gan ta ko ya samu wani bayani, don Allah a tuntubi Dr. Jamilu Runka (07060594659), ko Hajiya Hauwa’u (08143743638), ko Hajiya Jamila (07049708229).
Allah ya taimaka a same ta lafiya, Ameen.


