Wani bincike da jaridar Drop Site News ta fitar ya bayyana yadda gawurtaccen kawalin nan Jeffrey Epstein da tsohon Firaministan Isra’ila, Ehud Barak, suka yi…
Wani bincike da jaridar Drop Site News ta fitar ya bayyana yadda gawurtaccen kawalin nan Jeffrey Epstein da tsohon Firaministan Isra’ila, Ehud Barak, suka yi amfani da matsalolin tsaron Najeriya wajen neman kudi.
Binciken ya nuna cewa Epstein da Barak sun yi amfani da tashin hankalin Boko Haram a matsayin wata babbar dama da tazo musu ta kasuwanci, inda suka tallata fasahar leƙen asiri ga jami’an Najeriya.
Sun tallata na’urorin sanya idanu da aka gwada a kan Falasɗinawa wato tsarin biometric surveillance na kamfanin FST Biometrics ga gwamnatin Najeriya.
Ƙasar a wancan lokaci ta bayar da kwangilar aikin leƙen asiri ta yanar gizo wato internet surveillance ga kamfanin Elbit Systems na Isra’ila duk da adawar da wasu ‘yan majalisar Najeriya suka nuna.
Haka zalika binciken ya nuna cewa waɗannan yarjejeniyoyin tsaro sun kasance matakala ta tsoma hannu a tattalin arzikin Najeriya, musamman harkar man fetur da kuma tashoshin jiragen ruwa.
Ta hanyar Epstein, Barak ya samu damar halartar taron tsaron Najeriya ta yanar gizo da aka yi a Abuja cikin shekarar 2013, inda ya gana da tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan da manyan hafsoshin tsaro.
Ko da yake Barak ya nuna nadamar alaƙarsa da Epstein bayan bayyanar laifukan sa na lalata, amma rahoton binciken ya nuna cewa sun yi aiki kafaɗa da kafaɗa na tsawon sama da shekaru goma.
Kawo yanzu dai babu wani martani a hukumance daga hukumomin Najeriya game da waɗannan zarge-zarge da binciken Drop Site News ta bankado.
Aminya.


