Sani Gazas Chinade, Damaturu
Wasu al’ummomin Jihar Yobe Sun nuna gamsuwar su bisa ga yadda hukumar nan ta sake farfado da yankin arewa maso gabas (NEDC) ke gudanar da ayyukan raya kasa musamman kan abin da ya shafi gina hanyoyin mota da gyara wasu hanyoyin da suka baci, gina gidaje, asibitoci da makarantu tare da rarraba abinci ga masu kananan karfi hade da ‘yan gudun hijira.
Malam Umaru Muhammad wani mazaunin Damaturu ya bayyana cewar, “shi kan a iya sanin sa gwamnatin tarayya ba ta taba kafa wata hukuma ba da take taimakawa al’umma fiye da wannan hukumar ba ta NEDC da ke karkashin jajirtaccen shugaban ta Kuma babban shugaban ta Muhammad G. Alkali wadda sai dai mu yi godiya.”
Ya kara da cewar su a nasu ganin fa’idar wannan hukumar ga rayuwar su ya wuce na hukumar Kai daukin gaggawa na kasa NEMA duk da cewar ita hukumar ta NEMA Ita ma na taka muhimmiyar rawa wajen tallafawa al’umma amma duk da haka ga mu al’ummar Jihar Yobe, da sauran jihohin arewa maso gabas sai muce hukumar NEDC ta yi zarra wajen taimaka al’ummar yankin na arewa maso gabas duk da cewar da ma can gwamnatin tarayya ta kafa hukumar ne don kula da farfado da wannan yanki namu daga ifti’in ‘yan ta’adda da muka samu kan mu ciki na tsawon lokaci.
Haka nan a cewar shi kuma wani mazaunin karamar hukumar Nguru Malam Musa Ubaliyo cewa ya yi lalle wannan hukumar ta raya yankin arewa maso gabashin Najeriya. Northeast Development Commission. (NEDC) Karkashin Jagorancin Muhammad G. Alkali wanda kodinetan ta na Jihar Yobe. Farfesa Ali Ibrahim Abbas ya Jagoranta. sun cika alkawarin da suka dauka na kawo Jiragen ruwan zamani garin Garbi dake karamar hukumar Nguru.
A cewar sa a lokacin damina aka samu Iftila’in kifewar jirgin ruwa inda mutane da dama suka rasa rayukan su wanda ya taso daga garin Adiyani dake karamar hukumar Guri dake Jihar Jigawa zuwa Garin Garbi dake karamar hukumar Nguru a jihar Yobe.
A cewar sa ba tare da wani bata lokaci ba hukumar ta NEDC ta kawo Jiragen ruwan zamani guda biyu da rigunan Kariya (Life Jackets) na ruwa wanda za’a dinga sakawa idan za’a shiga Jiragen hadi da kayan abinci, tabarmi da sauran su domin a rabawa ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukan su a sanadiyar Kifewar Jirgin ruwan.
Amfanin rigunan shine, Allah ya kiyaye ko da an sami hatsarin Jirgin ruwan idan mutum yana da wannan rigar a jikin sa ba zai nutse cikin ruwan ba yana saman ruwan yana yawo har lokacin da za’a kawo masa agajin gaggawa.
Hukumar NEDCn sun mikawa Shugaban hukumar Agajin gaggawa na jihar Yobe SEMA. Dr. Mohammed Goje a hannun sa shi kuma ya mika kayan zuwa ga Shugaban karamar hukumar Nguru. Hon. Malam Muhammad Mairami wanda Sakataren karamar hukumar Hon. Ibrahim Muhammad (Oscar) ya wakilce shi.
Shi kuwa Alhaji Gambo Potiskum a nasa bangaren yabawa hukumar ta NEDC ya yi bisa ga yadda ta gina Musu katafariyar makarantar Firamare da Karamar sakandare irin ta zamani a Unguwar su ta Arikime wadda hakan ya sanya aka rage cunkoson daliban da abaya ake samu a makarantar Firamare ta Arikime wadda hakan babban abin burgewa ne.


