Daga: Sani Gazas Chinade , Damaturu
Shugaban hukumar alhazzan Jihar Yobe Alhaji Mai Aliyu Usman Biriri ya tabbatar da cewar, hukumar su ta kammala dukkanin Shirye-shiryen ta don gudanar da aikin hajjin bana na shekarar 2026 lura da yadda ta shirya dukan abin da ya dace don gudanar da wannan aiki ga dukkanin illahirin Mahajjatan Jihar su 1,337.
Alhaji Mai Aliyu Usman ya bayyana hakan ne cikin tattaunawar sa da wakilinmu dangane da yadda suka kammla shirye-shiryen su, kamar yadda hukumar alhazzan ta kasa NAHCON ta ba su umarni.
Shugaban ya kara da cewar a bana ma sun samu maniyyatan da suka cika dukkanin sharuddan hukumar su kimanin 1,337 wadda a halin da ake ciki sune adadin alhazzan da jihar ke da su waxanda in Allah ya sa za su tafi kasa Mai tsarki ta Saudi Arabiya don sauke farali a wannan shekara ta 2026 cikin adadin kujeru 1960 da aka baiwa Jihar.
Ya kara da cewar a halin da ake ciki a mako mai zuwa ne za su fara gudanar da alluran rigakafin cututtuka ga dukkanin illahirin mahajjatan su kamar yadda ya ke a bisa ga doka.
A cewar sa tun tunin sun fara gudanar da tarukan bita ga maniyyatan kamar yadda aka tsara a duk shekara ana yin hakan da nufin ilimantar da su ka’idodin yadda ake gudanar da aikin ibada na hajji tun daga kasa Najeriya har zuwa kasa mai tsarki ta Saudi Arabiya har ma kaiwa ga dawowar su gida.
Don haka shugaban na albishir ga dukkanin maniyyatan cewar, kamar dukkan shekara a wannan shekara ma hukumar su ta shirya tsaf don kula da harkokin su kana Ita Kuma gwamnatin Jihar ta tabbatar da cewar za ta cigaba da tallafa musu don su kai ga gudanar da ayyukan su na ibada cikin nasara kamar yadda aka saba yi a duk shekara.
Ya kara da cewar, yana tabbatar wa da maniyyatan cewar da zarar hukumar aikin hajji ta Kasa ta sanar da su ranakun da za a fara Jigilar su ya zuwa Kasa mai tsarkin su ma ba za su bata wani lokaci ba za su sanar da su akan lokaci.


