Saturday, April 11, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLafiyaUNICEF, EU Sun Horar Da 'Yan Jarida Kan Yaki da Rashin Abinci...

UNICEF, EU Sun Horar Da ‘Yan Jarida Kan Yaki da Rashin Abinci Mai Gina Jiki Ga Kananan Yara

Sani Saleh Chinade
Daga Damaturu

Hukumar UNICEF tare da hadin gwiwar kungiyar tarayyar Turai sun horar da ‘yan jarida kan yaki da karancin abinci mai gina jiki a fadin jihohi 3 na arewa maso gabas da suka hada da Borno, Adamawa, da Yobe (BAY).

Wannan taron horararwar ga manema labarai ta kwana daya da aka gudanar a zauren taro na otal din Sand Dune da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe a ranar Litinin 23 ga Maris 2026, ya tattaro wasu ‘yan jarida daga jihohi 3 na arewa maso gabas, da nufin inganta fahimtarsu kan yadda za a magance matsalolin da suka shafi rashin abinci mai gina jiki ga yara.

Wani bangare na tattaunawar ya kasance an gudanar da ziyarar gani da ido zuwa wasu cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko ta Gwange, inda ma’aikatan lafiya suka nuna amfani da fasahar su wajen gwaje-gwaje ga kananan yara kan abin da ya shafi ciyar da kananan yara abinci mai gina jiki wajen amfani da na’urar gwaji na tsakiyar hannu (MUAC) don tantance yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki.

Haka nan a cibiyar kula da lafiya a matakin farko ta Mairi Jami’an cibiyar sun nuna ka’idojin gwajin kananan yara da aka yi amfani da su don tantance kananan yara marasa lafiya sakamakon rashin abinci mai gina jiki tattare da su.

Bayan haka, tawagar ‘yan jaridar Hadiza Maina Adamu, jami’ar abinci mai gina jiki ta jihar Yobe ta jagoranta, wajen ziyartar wani rumbun adana magunguna da abinci mai gina jiki ga kananan yara dake fama da tamowa, inda ta nuna sama da kwalaye 3,264 na abincin da aks shirya don amfani da shi (RUTF), wadda wani muhimmin kayan abinci ne da ake amfani da shi wajen kula da yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki tamuwa.

Da ya ke magana ta hanyar kafar sada zumunci ta (Zoom), yayin tattaunawar, Manajan abinci mai gina jiki ga kananan yara na UNICEF Joseph Senesie ya jaddada cewa lokacin rashin abinci mai gina jiki ga kananan yaran ya fara ne daga watan Mayu zuwa Satumba, yawanci ya kan haifar da qaruwar matsalolin rashin abinci mai gina jiki mai tsanani wadda ke nuna alamu na farko.

Joseph Senasie ya kuma bayyana fatan cewa alkaluman wannan shekarar ba za su wuce matakan da suka gabata ba, yana mai yaba wa goyon bayan hukumar tarayyar turai EU don ba da damar magance adadin yara sama da 40,000 a cikin jerin shirye-shiryen da suka gabata.

A jawabinta, Jami’ar abinci mai gina jiki ga kananan yaran ta Jihar Yobe, Hadiza Maina Adamu, ta ba da cikakken bayani game da halin da ake ciki a yanzu, tana mai cewa jihar tana cikin mataki na 3 na rarraba tsarin tsaron abinci mai gina jiki na (IPC), wanda ke nuna babban matakin tsaron abinci.

Hadiza ta jaddada cewa rashin abinci mai gina jiki mai tsanani na duniya (GAM) ya kai kashi 10.8% bisa ga bayanan sa ido na 2025, wanda ya karu daga kashi 14% a shekarun baya, kodayake adadin ya kasance mai matukar muhimmanci.

A cewarta tun daga 2010, ayyukan jinya sun fafada sosai har sun hada da wuraren shirin kula da marasa lafiya a ciniyoyi 306 (OTP), na kwantar marasa lafiya, da kuma wuraren shirin ciyar da abinci mai gina jiki guda 120 (TSFP).

A lokacin gabatar da makalar sa, Dakta Babagana Kundi Machina, babban sakataren hukumar Kula da lafiya a matakin farko na Jihar Yobe, ya jaddada cewa tallafin EU ya taimaka wajen tabbatar da samar da abinci da madara mai magani ba tare da katsewa ba, wanda hakan ya saukaka matukar gaske musamman wajen jinyar yaran da ke fama da tamuwa a cikin al’umma a fadin jihar baki daya.

Masu ruwa da tsaki kan harkokin kiwon lafiya na Jihar, sun bayyana hadin gwiwa tsakanin UNICEF, hukumar agajin jin kai ta tarayyar Turai, da gwamnatocin jihohin BAY a matsayin muhimmin abu don ci gaba da tallafawa wajen bada tallafin abinci mai gina jiki a tsakanin yaran don fuskantan kalubalen jin wai masu sarkakiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments