Monday, April 13, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeSiyasaMagoya Bayan Sanata Bomai Sun Mara Masa Bayan Takarar Gwamnan Yobe A...

Magoya Bayan Sanata Bomai Sun Mara Masa Bayan Takarar Gwamnan Yobe A 2027

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Kungiyar magoya bayan Sanata Ibrahim Bomai Sun nuna goyon bayan su ga Sanatan don fitowa ya tsaya takarar gwamnan Jihar Yobe a inuuwar Jam’iyyar APC a zaben da ke tafe a shekarar 2027.

Dandazon kungiyoyi magoya bayan Sanata sun bayyana hakan ne a ranar asabar a yayin da suka taru a farfajiyar Kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya da ke garin Damaturu don bayyana wannan bukata ta su.

Sanata Ibrahim Mohammed Bomai shi ke wakiltar mazabar kudancin Jihar Yobe a majalisar dattawa ta kasa wadda karo na biyu ke nan yana wakiltar al’ummar mazabar sa a majalisar dattawan ta kasa.

A cikin jawabin su dubban magoya bayan Sanata Bomai da suka fito daga kowane yanki na Jihar Yobe Sun bayyana bukatar su don Sanatan ya fito don tsayawa takarar gwamnan a shekara mai zuwa ta 2027 don ya dora daga yadda gwamna mai ci Dr Mai Mala Buni zai tsaya akai kasancewar shi ne kadai zai iya gudanar da mulkin Jihar ba tare da fuskantar barazanar samun koma baya ba.

Alhaji Muhammad Ngordi wani babban jigo a Jam’iyyar ta APC daga mazabar Jihar Yobe ta gabas (zone A) ya bayyana cewar, ai su ba su da wani dan takarar da ya wuce Sanata Ibrahim Bomai in lokaci ya yi domin shi ne daya tilo da ya ke gudanar ayyuka a yankin mazabar sa da ya karade ko’ina da hanyoyin mota da makamantan su.

A cewar sa don haka ne ma suka fito kwai da kwarkwata don nuna goyon bayan su ga Sanatan don ya tfito ya tsaya takarar gwamnan da zarar lokacin ya yi.

Shi kuwa Alhaji Salisu Bakabe wadda tsohon Kwamishina ne a Jihar ya Yobe cewa ya yi ai goyon bayan Sanata Bomai da ya fito don tsayawa takarar gwamnan a zaben da ke tafe a shekarar 2027 ya zama ma wajibi domin ko ba komai Sanatan ya nuna shi wakili ne nagari ga al’umma musamman in aka duba irin ayyukan da ya ke gudanar da ayyukan da suka shafi gina hanyoyin mota, tallafawa daliban ilimi tare da dibar wasu ya zuwa kasashen ketare don karo ilimi a dukkannin illahirin kananan hukumomi 4 da ke mazabar sa ta kudancin Yobe.

Shi ma wani jagora a kungiyar goyon bayan Sanata Bomai don fitowa takarar Gwamna a Jihar Yobe daga Geidam Hafiz Yusuf Gaidam nuna goyon bayan kungiyar su ya yi na fitowa takarar Sanatan don tsayawa takarar gwamnan a 2027 domin ko ba komai shine kadai zai iya fitar da kitse a wuta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments