Daga Sani Gazas Chinade Damaturu
Hukumar raya yankin arewa maso gabas (NEDC) ta kaddamar da aikin gina hanya mai nisan kilomita 2.5 da gadoji biyu a ƙaramar hukumar Potiskum ta jihar Yobe.
Manajan daraktan NEDC, Alhaji Muhammad Goni Alkali, ya kaddamar da aikin yayin da yake miƙa takardar yarjejeniyar gudanar da aikin ga Kamfanin Eighteen (EEC) da ke Potiskum.
Manajan daraktan wanda kodinetsn hukumar na Jihar Yobe, Farfesa Ali Ibrahim Abbas, ya wakilta ya ce, idan aka kammala aikin zai haɗa al’ummomin Kara, Masaka, da Mazaga, tare da gada ɗaya “wanda zai magance matsalolin shiga Tandari cikin garin Potiskum na dogon lokaci”.To
A cewarsa, shirin yana goyon bayan umarnin NEDC bayan murmurewa da sake tsugunar da jama’a, yana mai jaddada cewa aikin zai haɓaka sufuri mai aminci na kayayyaki, samun damar zuwa cibiyoyin kiwon lafiya, makarantu, kasuwanni, da rayuwa, wanda zai haifar da ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a Potiskum da maƙwabta.
“Kammala aikin zai ɗaga darajar tattalin arzikin mazauna yankin da kuma samar da ayyukan yi ga masu sana’o’i, da ma’aikata da Kuma Inganta tattalin arzikin yankin baki daya,” in ji shi.
Da yake mayar da martani, wakilin kamfanin EEC a wurin taron, Mista Gao Kun ya yi alƙawarin kammala ayyukan cikin lokaci cikin watanni 10, yana mai alƙawarin cika dukkan ƙa’idodi.
Ana iya tunawa cewa a farkon shekarar da ta gabata, shugaban NEDC, Mohammed G. Alkali, tare da dakta Abubakar Garba Iliya, babban daraktan gudanarwa da kuɗi na hukumar ta NEDC sun duba wasu wuraren da ake buƙatar kayayyakin more rayuwa a Jihar Yobe kuma sun yi alƙawarin aiwatar da su


