Daga Sani Gazas Chinade Damaturu
Sojojin rundunar hadin gwiwa (Arewa maso Gabas) Operation HADIN KAI (OPHK) a karkashin Operation DESERT SANITY sun sami wata babbar nasara a kokarin da ake yi na lalata hanyoyin samar da kayayyaki da hanyoyin tallafawa laifuka a Arewa maso Gabas.
A cewar wata sanarwa da jami’in yada labarai na hedikwatar rundunar hadin gwiwa (Arewa maso Gabas) Operation HADIN KAI Laftanar Kanar Sani Uba, wanda ke aiki bisa ga bayanan sirri a ranar 23 ga Janairu 2026, sojoji sun kama wata da ake zargi da sayar da miyagun kwayoyi, Hauwa Abulazeez, mai shekaru 65, a karamar hukumar Askira Uba da ke jihar Borno.
Ya ce ana zargin wannan mata a matsayin daya daga cikin masu samar da tabar wiwi ga ‘yan Boko Haram ‘yan ta’adda da ke aiki ta hanyar Askira Uba, Rumirgo, Gwahi, Wamdiyo, Uvu, da Gaya, da kuma wata babbar hanyar rarrabawa miyagun kwayoyi a cikin al’ummomi da dama.
“Binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ta samo haramtaccen abu ne daga karamar hukumar Sarti Baruwa ta jihar Taraba kuma ta Yi jigilar su ta hanyoyin samar da kayayyaki da aka tsara don rarrabawa ga al’umma.”
“A lokacin aikin, an gano kwalayen kwayoyin cannabis guda 14 da aka matse, tare da jimlar nauyinsu na kimanin kilo 30.
Ya kara da cewa wanda ake zargin tana tsare a yanzu haka ana gudanar da bincike na farko, yayin da ake ci gaba da daukar matakai na gano da wargaza babbar hanyar sadarwa da suke amfani da su a safarar da rarraba muggan kwayoyin.
“Wannan mataki na nuna tasirin hana hanyoyin samar da kayayyaki ba bisa ka’ida ba wadanda ke haifar da tashin hankali, aikata laifuka, da rashin kwanciyar hankali ta hanyar wargaza wadannan hanyoyin sadarwa, aikin yana taimakawa wajen inganta yanayin tsaro, rage tasirin laifuka, da kuma karfafa iko wajen samar da doka oda a duk fadin yankin.
“OPHK ta ci gaba da jajircewa wajen tunkarar da kuma kawar da duk wani nau’in laifuka a fadin Arewa maso Gabas ta hanyar ci gaba da ayyukan leken asiri da kuma ci gaba da matsin lamba a tsakanin sojoji yadda za su ci gaba da hana cibiyoyin aikata laifuka har sai an cimma zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa,” in ji sanarwar a wani bangare.


