Sunday, April 12, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiYan Sanda Sun cafke Mai Safarar Kwayoyi A Borno 

Yan Sanda Sun cafke Mai Safarar Kwayoyi A Borno 

Daga Sani Gazas Chinade Damaturu

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta kama wata mata ‘yar shekara 22 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, sannan ta kwato katuna (sachets) Tramadol guda 89 a wani samame da ta yi a Maiduguri.

Kamar yadda rahoton ke nuna wa an kama wannan matar ne a ranar 20 ga Janairu, 2026, bayan samun sahihan bayanai daga jami’an tsaro, a cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, ASP Nahum Kenneth Daso, ya fitar a madadin Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Naziru Abdulmajid.

‘Yan sanda sun ce jami’an tsaro da ke aiki a Sashen leken asiri na Jihar sun kama wanda ake zargin da misalin karfe 7:30 na yamma a tashar motar da ke kan titin Baga.

“An same ta da bakar jakar fata dauke da masara da aka nika, wadda aka boye katunan Tramadol guda 89 a ciki,” in ji Daso.

Binciken farko ya nuna cewa an yi zargin cewa kawunta ne ya mika wa wanda ake zargin kwayoyin domin a kai su karamar hukumar Damasak, inda ya kara da cewa wannan ne karo na biyu da take yin irin wannan aikin.

Wanda ake zargin da kuma Kayan aka gano suna hannun ‘yan sanda a halin yanzu, yayin da ake ci gaba da kokarin kama wanda ke da hannu a cikin bada kayan.

Daso ya kuma nanata alkawarin rundunar na yaqi da safarar miyagun kwayoyi, shan muggan kwayoyi da sauran ayyukan laifuka da ke haifar da aikata munanan laifuka a jihar.

Don haka rundunar ta yi kira ga mazauna yankin da su tallafa wa ‘yan sanda da bayanai masu inganci a kan lokaci ta hanyar layukan gaggawa da rundunar ke da su. 0806 807 5581 da 0802 347 3293.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments