Daga Sani Gazas Chinade Damaturu
Mai martaba Sarkin Funakaye, Yakubu Muhammad Kwairanga na IV, dake Jihar Gombe, ya ba Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, sarautar gargajiya ta Dikuma na Funakaye, a lokacin ziyarar martabawa ga basaraken a fadarsa da ke Bajoga,Jihar Gombe.
An yi taron ne a ranar talata, 17 ga Fabrairu, 2026, a cewar wata sanarwa da Darakta Janar na ‘yan Jarida da harkokin yada labarai na gwamna Buni, Mamman Mohammed ya fitar.
Sarkin da kansa ya gabatar da takardar nadin ga gwamnan a fadar, yana mai ambaton cancanta da kuma hidimar da Buni ya ke yiwa al’umma a matsayin tushen girmamawar.
A cewar sanarwar, sarkin ya sanya hannu kan takardar nadin kuma ya bayyana gwamnan a matsayin wanda ya cancanci wannan sarautar gargajiya mai daraja.
Buni, wanda tuni ya ke riqe da sarautun gargajiya da dama a faxin arewacin Najeriya, ya qara da Dikuma na Funakaye a cikin jerin sunayen sarautun da aka ba shi.
Sauran mukaman Sarautun gargajiyar da gwamnan ke riqe da su sun hada da Ciroman Gujba, Walin Damaturu, Zannah Yaudima na Ngelzarma, Baraden Fika, Zannah Gadama na Machina, Sardaunan Fune, Matawalle na Gudi da Yeriman Pataskum.
Bikin ya ja hankalin jami’an fadar da wasu Jami’an gwamnati, wanda ke nuna wani amincewa da alakar gwamnan da cibiyoyin gargajiya a yankin.


