Daga, Sani Gazas Chinade Damaturu
Majalisar tsaron jihar Yobe karkashin jagorancin gwamna Mai Mala Buni, ta yaba wa al’ummar jihar kan yadda suka gudanar da ayyukansu cikin kwanciyar hankali a lokacin zaben fidda gwanin majalisun tarayya biyu na jam’iyyar da aka gudanar zuwa yanzu.
Da yake magana da manema labarai Jim kadan bayan fitowa daga taron, kwamishinan ‘yan sanda na jihar Yobe, Usman Kamfani Jibrin, ya ce majalisar ta shawarci duk wani mutum ko wata kungiya da bata gamsu ba da abin da aka yi ba da ta nemi hakkinta bisa doka da kuma ta hanyar hukumomin da aka kafa don kula da koken jama’a kan lamarin.
Ya ce hukumomin tsaro suna cikin shiri sosai kuma za a magance duk wani yunkuri na kawo cikas ga zaman lafiyar jihar, yana mai cewa, duk wani mutum ko wata kungiya da ke da hannu a daukar nauyin ko shiga harkar tada hankali na siyasa ko ta’addanci za ta fuskanci fushin doka.
A cewar kwamishinan, jami’an tsaro sun gano shirin da wasu ‘yan siyasa ke yi na shigo da ‘yan daba cikin jihar don haifar da rudani “muna aiki kan gano masu daukar nauyin da duk wanda ke da hannu a ciki”.
Ya kuma gargadi dukkan ‘yan siyasa game da gangamin siyasa, yana mai cewa, “akwai jadawalin kowane aiki na siyasa kuma lokaci bai yi ba tukuna don gangamin siyasa”.
A wani ci gaba kuma, an shawarci jama’a da su kasance masu lura da motsin duk wani bako ko mutune a cikin al’ummominsu.
Mai ba gwamna shawara kan harkokin tsaro, Birgediya janar, Dahiru Abdulsalam (rtd) ya ba da shawarar cewa, masu laifi a halin yanzu suna tserewa sakamakon ayyukan soji a cikin daji don neman mafaka.
“Ya kamata jama’a su ba da rahoton shigar wasu mutanen da ba su gamsu da kasancewar su a cikin su da kewayen yankunansu ba, kuma duk wanda aka samu yana boye masu laifi za a kama shi kuma doka ta yi aiki akan sa” in ji Abdulsalam.


