Daga, Sani Gazas Chinade Damaturu
Majalisar Zartarwar ta Jihar Yobe (EXCO), karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni, wanda mataimakinsa, Hon. Idi Barde Gubana (Wazirin Fune) ya wakilta, ta amince da kashe jimillar naira biliyan 59.8 don muhimman ayyukan ci gaba a fadin jihar.
Taron, wanda aka gudanar a ranar Litinin a zauren majalisar da ke gidan gwamnati jihar da ke garin Damaturu, ya tattauna kan muhimman batutuwan da suka shafi jihar, ciki har da samar da kayayyakin more rayuwa, samar da kayayyakin samar da kiwon lafiya, makamashi, kasuwanci, ci gaban wasanni, tsaro da sauran su.
A cikin jawabinsa, mataimakin gwamna, wanda ke wakiltar gwamna, ya yaba da kokarin da gwamnati ke yi na inganta tsaron abinci da kuma ci gaba da samar da kayayyakin more rayuwa.
Ya kuma bukaci ‘yan jihar da su ci gaba da tallafawa shirye-shiryen gwamnati da kuma yin addu’a don samun zaman lafiya da shirye-shirye masu tasiri.
Bayanin amincewar ya nuna cewa an ware Naira biliyan ₦34.1 don gina hanyoyi, ciki har da titin Kaliyari-Bayamari mai tsawon kilomita 59 da ya ratsa kananan hukumomin Tarmuwa da Bursari, da kuma titin Bayamari-Gaidam mai tsawon kilomita 53 wanda ya haɗa Bursari da Gaidam.
[28/04, 10:14 am] Muhammad Sani Chinade Yobe: A fannin kasuwanci, an amince da Ware Naira biliyan ₦8.58 don gina sabuwar zamani ta Jajimaji, da kuma ayyukan waje a kasuwannin zamani na Machina da Buni-Yadi.
Majalisar ta kuma amince da Ware Naira biliyan ₦5.35 don ayyukan sufuri da makamashi, wanda ya shafi siyan janareton wutar lantarki, shigar da kebul masu sulke a ƙarƙashin ƙasa a Gidan Gwamnati, da kuma sanya fitilun titi 2,200 masu amfani da hasken rana a hedikwatocin kananan hukumomi 11.
Sauran ayyukan sun haÉ—a da gina layin wutar lantarki mai karfin 33KV daga Bukarti zuwa Kanamma da kuma samar wa da gina tashoshin rarraba wutar lantarki transfoma da hanyoyin rarrabawa a Kanamma.
An Samar da tallafin kula da lafiya na Naira biliyan ₦5.54 don gina sabon ginin ofis na Ma’aikatar Lafiya da Ayyukan Jama’a da ke hedikwatar Hukumar Gudanar da Asibitoci, da gyaran asibitoci na gaba É—aya a Damagum da Nangere, da kuma shigar da kayan aikin haÆ™ori a Asibitin Ƙwararru na Jihar Yobe dake Damaturu. Za a kuma samar da Æ™arin janareto ga manyan asibitoci a faÉ—in jihar.
A ɓangaren wasanni, an amince da Naira biliyan ₦3.35 don ƙarin ayyuka kan sake ginawa da haɓaka filin wasa na 27 ga Agusta da ke Damaturu.
Majalisar ta sake nanata alÆ™awarinta ga manufofi da shirye-shirye da nufin inganta yanayin rayuwa na al’ummar jihar ta Yobe.


