Saturday, June 13, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiFALALAR ZULHIJJA DA MUHIMMANCIN LAYYA TARE DA SHEIKH NURA HARUNA DAURA

FALALAR ZULHIJJA DA MUHIMMANCIN LAYYA TARE DA SHEIKH NURA HARUNA DAURA

Daga: Bashar Isah Daura

Wani malamin addinin Musulunci a Jihar Katsina, Sheikh Nura Haruna Daura, ya yi tsokaci kan muhimmancin ibadar layya da falalar kwanaki goma na farkon watan Zulhijja, inda ya jaddada bukatar Musulmi su kara himma wajen ibada da ayyukan alheri a wannan lokaci mai albarka.

Sheikh Nura Haruna Daura ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu Bashar Isah Daura, inda ya ce kwanaki goma na farkon watan Zulhijja na daga cikin ranaku mafiya daraja a Musulunci, saboda irin falala da lada da Allah Ya tanadar wa bayinsa masu aikata ayyukan alheri a cikinsu.

Ya ce ya kamata Musulmi su yi anfani da wannan dama wajen yawaita ibadu kamar nafila, azumi, karatun Alkur’ani Mai Girma, zikiri, istigfari da kuma taimakon marasa karfi, domin neman kusanci ga Allah Madaukakin Sarki.

Dangane da ibadar layya kuwa, Sheikh Nura Haruna Daura ya bayyana cewa layya na da matukar girma da falala a Musulunci, inda ya ce girman ibadar yanka layya ya fi girman ibadar yanka abin suna ta fuskar asali da falala.

Ya kara da cewa kowane Musulmi mai hali zai iya yin layya, mace ko namiji, saurayi ko budurwa, muddin yana da ikon gudanar da ita bisa koyarwar addinin Musulunci.

Malamin ya kuma yi kira ga Musulmi da su gudanar da ibadar cikin tsoron Allah da kyakkyawar niyya, tare da raba wa mabukata da marasa karfi domin kara dankon zumunci da taimakon juna a tsakanin al’umma.

Haka kuma ya bukaci al’umma da su ci gaba da addu’o’i domin samun zaman lafiya da ci gaban kasa, tare da neman Allah Ya karbi ibadun Musulmi a wannan wata mai albarka.

Bashar Isah Daura

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments