Daga Sani Gazas Chinade Damaturu
Hukumar raya arewa maso gabas (NEDC) ta bayyana shirye-shiryen sake gina titin Damaturu–Gujba–Magza mai tsawon kilomita 77.
Manajan Daraktan Hukumar, Muhammad Goni Alkali ne, ya bayyana hakan ga manema labarai a lokacin kaddamar da sake ginawa da kuma shimfida kwalta na titin Damaturu–Gujba–Buni Yadi zuwa Magza kan iyakar Jihar Yobe da Borno.
Goni Alkali ya bayyana hanyar a matsayin hanya mai matukar muhimmanci da ta hada jihohin Yobe, Borno, Adamawa da Taraba.
Ya jaddada cewa bayan kammala aikin titin mai tsawon kilomita 77 zai inganta sake hadewar yankuna, inganta hadin gwiwa tsakanin tsaro, da kuma inganta harkokin kasuwanci da noma tsakanin jihohin.
Shugaban NEDC ya ce aikin zai kara karfafa kokarin da ake yi na sake gina ababen more rayuwa, da kuma bunkasa ci gaban tattalin arziki a fadin jihar Yobe da kuma yankin arewa maso gabas baki daya.
“Mun kuduri aniyar sake gina wannan hanyar, mun fara mataki na farko, wanda ya shafi hanyar Damaturu–Gujba–Buni Yadi–Magza mai nisan kilomita 77.
“Bayan mun kammala matakin farko, za kuma mu aiwatar da mataki na biyu na aikin, wanda ya shafi sauran yankin Magza zuwa Biu a Jihar Borno mai nisan kilomita 51 wadda dukkan hanyar motar daga Damaturu zuwa Biu na da nisan kilomita 128.”
“Ina so in tabbatar wa mutanen jihohin Yobe da Borno cewa NEDC za ta tabbatar da kammala wannan hanyar cikin nasara ba tare da wata matsala ba ko kuma tsayawa ba,” in ji shi.
A cewarsa, hukumar ta sanya fitilun titi sama da 6,000 masu amfani da hasken rana a fadin kananan hukumomi 17 na Jihar Yobe.
Ya kuma bayyana cewa, a kokarin magance karancin ruwa a jihar, NEDC ta gina rijiyoyi sama da 150 a fadin Yobe.
Tun da farko, Gwamna Mai Mala Buni na Jihar Yobe, wanda ya kaddamar da aikin, ya ce sake gina hanyar ya yi dai-dai da jajircewar gwamnatinsa ga ci gaban kayayyakin more rayuwa.
Ya sake tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Yobe a karkashin jagorancinsa ta ci gaba da jajircewa wajen ci gaban kayayyakin more rayuwa da kuma kokarin farfado da tattalin arziki bayan rikicin ‘yan Boko Haram da Jihar ta yi fama da shi .


