Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Dangane da bala’in ambaliyar ruwa da ya addabi kananan hukumomin Maiduguri da Jere a kwanakin baya, UNICEF tare da hadin gwiwar gwamnatin jihar Borno, da hukumar kula da lafiya matakin farko (PHCDA) da sauran abokan hulda, sun kaddamar da kamfen na allurar rigakafin cutar kwalara, rigakafin kyanda, da kuma na sinadarin Vitamin A.
Shugabar ofishin UNICEF na Maiduguri, Misis Christina Valderrama Maya – Alfirev, ta jaddada muhimmancin wadannan matakan wajen tabbatar da makomar yara da kuma inganta lafiyar al’umma.
“A madadin dukkan jami’an mu hade da abokan hulda akan harkokin kiwon lafiya da samar da abinci mai gina jiki, muna yaba wa shugabannin gwamnatin jihar Borno bisa gaggawar da ta yi wajen dakile illar bala’in ambaliyar ruwa da ya afku a Maiduguri,” in ji ta.
Christina ta bayyana tsananin cutar kwalara, kyanda, da karancin sinadarin bitamin A, inda ta jaddada bukatar yin alluran rigakafi akan lokaci don kaucewa yaduwar su.
“Cutar kwalara cuta ce mai muni da za ta iya haifar da mutuwa cikin sa’o’i idan ba a kula da ita ba. Kyanda cuta ce mai saurin yaɗuwa wacce ke haifar da munanan matsalolin lafiya, gami da ciwon huhu yayin da karancin sinadarin bitamin A na iya haifar da makanta da kuma kara saurin kamuwa da cututtuka,” in ji ta.
A jawabinsa Kwamishinan lafiya na jihar Borno, Farfesa Malam Baba Gana, ya tabbatar da bullar cutar kwalara a Maiduguri tare da jaddada kokarin gwamnatin jihar na inganta lafiyar al’ummarta.
Farfesa Gana ya shawarci iyaye da su kai ‘ya’yansu asibiti mafi kusa domin a yi musu alluran rigakafi sannan ya ja hankalin manya da su rika zuwa domin samun ruwan sha mai tsafta.
Wakilin hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya (WHO) a jihar Borno, Dr. A. Telezeou, ya yabawa abokan hadin gwiwa da gwamnati bisa goyon bayan da suke badawa , inda ya bada tabbacin ci gaba da ba gwamnati da al’ummar jihar Borno goyon baya.
Babban Sakataren hukumar lafiya a matakin farko (PHCDA) a Jihar Borno, Farfesa Mohammed Alhaji
ya yi kira ga iyaye da shugabannin al’umma da su hada ’ya’yansu da na makwabta domin zuwa asibitoci da wuraren da aka kebe domin yin alluran rigakafi.
Ya ba da tabbacin cewa magungunan ba su wata matsala sakamakon an gwada su kuma hukumomin da abin ya shafa sun amince da ingancin su.


