Na yi wannan kira ne a yayin ganawarmu da jakadun ƙasashen Tarayyar Turai da kuma manyan abokan hulɗar mu na ƙasashen waje a lokacin ziyararsu a Jaharmu ta Katsina domin taya murnar bukukuwan Ƙaramar Sallah na wannan shekara ta 2026. Tattaunawar ta yi armashi sosai, domin an mai da hankali kan ƙarfafa haɗin gwiwa da inganta mu’amala da kuma samar da sababbin damarmaki domin samun ci gaba mai ɗorewa da wadata a Jaharmu.
Na sake jaddada anniyar gwamnatinmu na gudanar da tsarin mulki mai tafiya tare da kowa. Tsari ne da yake ba da muhimmanci ga samar da ci gaba mai ɗorewa. Tsari ne da yake fifita bunƙasa tattalin arziki da daidaito wajen rabon arzikin bisa adalci ga al’ummarmu. Muna ƙoƙarin samar da yanayin da ya dace da kasuwanci; inda zuba jari zai yawaita; haɗin gwiwa zai ƙarfafa domin a samu sababbin hanyoyin inganta rayuwa.
A yau, Jiharmu ta Katsina tana cikin jahohin da suke sahun gaba a Najeriya waɗanda suka fi dacewa domin zuba jari da haɗin gwiwa, musamman a fannonin noma da ilimi da fasaha da ƙere-ƙere da kuma ƙarfafa mata. Tsarinmu na tafiya tare da kowa a dukkan shirye-shiryenmu yana tabbatar da cewa ci gaban da ake samu yana tasiri ga dukkan al’ummarmu; ci gaban a hannunsu yake, don haka suke tabbatar da ɗorewarsa.
Ina samun ƙwarin gwiwa daga yadda abokan hulɗarmu suke nuna sha’awarsu gare mu tare da jajircewarsu. Da yardar Allah, wannan tattaunawa za ta haifar da ayyuka a zahiri waɗanda za su inganta rayuwar jama’armu, su ƙarfafa tattalin arzikinmu, tare da ɗaga darajar Jaharmu.
Fassara daga Mannir Wurma Ph.D,
Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Gwamnatin Jihar Katsina


