Wednesday, April 15, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamnatin Yobe Ta Raba Babura 200 Ga Ma'aikatan Aikin Gona 

Gwamnatin Yobe Ta Raba Babura 200 Ga Ma’aikatan Aikin Gona 

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamnatin jihar Yobe ta raba babura guda 200 ga ma’aikatan aikin gona domin gudanar da ayyukan kula da harkokin noma a jihar.

Kwamishinan ma’aikatar gona da albarkatun kasa Hon Ali Mustapha Goniri ne ya bayyana haka a lokacin da yake mika baburan ga wadanda suka amfana.

Ya ce rabon baburan  hawa 200 an yi shi ne don tallafawa ayyukan su da kuma bunkasa noman zamani a jihar ta hanyar sabbin dabaru da kayan aiki, tare da tallafawa ma’aikatan aikin gona.

Goniri ya ce ma’aikatar gona za ta sa ido kan yadda ma’aikatan da ke aikin fadada ayyukan noma ke yi domin tabbatar da cewa manoma a kowane lungu da sako na jihar suna noman amfanin gona da iri masu inganci.

A cewarsa, an horas da ma’aikatan da za su yi aiki a matsayin yadda za su kyautata alaka tsakanin masu bincike da manoma, don habaka samar da kayayyaki, tabbatar da samar da abinci, da kuma inganta rayuwar manoma.

A nasa jawabin, babban sakataren ma’aikatar Muhammad Inuwa Gulani, ya ce ma’aikatan ma’aikatar  aikin gona za su taimaka wa manoma wajen yanke shawara kan kirkire-kirkire da fasaha kan harkokin noma na zamani.

Ya ce ma’aikatan za su kuma taimaka wa manoma wajen samun sabbin bayanai da fasahohin zamani, inda ya ce shirin zai taimaka wa manoman wajen inganta sana’o’insu, da inganta rayuwar su, da tabbatar da samar da abinci ga al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments