Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnatin jihar Yobe ta raba babura guda 200 ga ma’aikatan aikin gona domin gudanar da ayyukan kula da harkokin noma a jihar.
Kwamishinan ma’aikatar gona da albarkatun kasa Hon Ali Mustapha Goniri ne ya bayyana haka a lokacin da yake mika baburan ga wadanda suka amfana.
Ya ce rabon baburan hawa 200 an yi shi ne don tallafawa ayyukan su da kuma bunkasa noman zamani a jihar ta hanyar sabbin dabaru da kayan aiki, tare da tallafawa ma’aikatan aikin gona.
Goniri ya ce ma’aikatar gona za ta sa ido kan yadda ma’aikatan da ke aikin fadada ayyukan noma ke yi domin tabbatar da cewa manoma a kowane lungu da sako na jihar suna noman amfanin gona da iri masu inganci.
A cewarsa, an horas da ma’aikatan da za su yi aiki a matsayin yadda za su kyautata alaka tsakanin masu bincike da manoma, don habaka samar da kayayyaki, tabbatar da samar da abinci, da kuma inganta rayuwar manoma.
A nasa jawabin, babban sakataren ma’aikatar Muhammad Inuwa Gulani, ya ce ma’aikatan ma’aikatar aikin gona za su taimaka wa manoma wajen yanke shawara kan kirkire-kirkire da fasaha kan harkokin noma na zamani.
Ya ce ma’aikatan za su kuma taimaka wa manoma wajen samun sabbin bayanai da fasahohin zamani, inda ya ce shirin zai taimaka wa manoman wajen inganta sana’o’insu, da inganta rayuwar su, da tabbatar da samar da abinci ga al’umma.


