Daga Sani Gazas Chinade Damaturu
Sanata mai wakiltar Borno ta tsakiya, Kaka Shehu, ya tallafa wa mazabarsa da tallafin kayayyakin sana’o’i kudade a wani shiri nasa na karawa talakawan mazabarsa tallafin Inganta rayuwa.
Wannan shirin bada tallafin kimanin al’ummar mazabarsa 3,092 ne za su cu gajiyar tallafin a fadin kananan hukumomi takwas na majalisar dattawan Jihar Borno ta tsakiya.
Daga cikin wadanda za su ci gajiyar tallafin, mutane 2,592 daga cikin su ne za su karbi kayayyakin karfafawa iri-iri da suka hada da kananan motocin Hijet, Keke Napep, injinan ban ruwa, injinan dinki da nika, injinan ruwa masu amfani da hasken rana da injinan, zuba taki da injunan girbin shinkafa, da sauran kayayyakin aikin gona.
Yayin da sauran mutane 500 da za su ci gajiyar tallafin za su sami tallafin tsabar kudi kimanin ₦100,000 kowannensu don tallafa wa sana’o’insu.
Gwamna Zulum a wajen bikin kaddamar tallafin a gidan gwamnati ya yabawa sanata Kaka Shehu bisa yadda yake kokari wajen inganta rayuwar al’ummar mazabar sa da kuma irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban jihar Borno.
“Wannan ba shi ne karon farko da Sanata Kaka Shehu ke raba kayan karfafawa ga jama’ar mazabar sa ba.in ji zulum.
Gwamna Zulum ya kuma bayyana irin tasirin da sanatan ya yi a aikin majalisa, inda ya ce a cikin shekaru biyu kacal Sanatan ya dauki nauyin kudirori masu muhimmanci da suka hada da na kafa jami’ar kasuwanci da aikin gona ta tarayya da ke Bama da kuma cibiyar kiwon lafiya ta tarayya a jihar Borno.
Zulum ya kara da cewa, “Ina son in yaba masa ba wai kawai saboda yadda ya rika bada gudummawa a majalisar dattawa ba, har ma da irin rawar da ya taka a majalisar dattawa, wadannan gudunmawar da ba a taba samu ba a tarihin jiharmu.”
Ya kuma bukaci sanatan da ya ci gaba da kokarinsa tare da ba shi tabbacin ci gaba da ba shi goyon bayan gwamnati da al’ummar jihar Borno.
Da yake mayar da martani, Sanata Kaka Shehu ya sanar da cewa duk wanda ya ci gajiyar abubuwan da aka bayar na kayan aiki zai kuma samu karin tallafin kudi na naira 20,000.
Ya kuma bayyana bayar da gudunmawar teburan makaranta guda 450 da za a raba wa makarantun gwamnati da ke yankin majalisar dattawan sa.
“Ina matukar godiya da jagorancin Gwamna Zulum a jihar, wannan shine kashi na biyu na shirin tallafi don karfafawa jama’a, kuma ina kira ga duk wadanda suka amfana da su yi amfani da wadannan kayayyaki yadda ya kamata.
“Ina Kuma tabbatar muku da cewa wannan shiri zai dore,” in ji Sanata Lawan.
Taron ya samu karramawa daga mataimakin gwamna Umar Kadafur; ‘yan majalisar dokokin jiha; Sakataren Gwamnatin Jiha; Shugaban Ma’aikata; Mukaddashin Shugaban Ma’aikata; Kwamishinonin; Shugabannin Kananan Hukumomi; masu ba da shawara na musamman; jiga-jigan APC; da sauran manyan masu ruwa da tsaki na Jihar.


