Wednesday, April 15, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiRashin Tsaro: Zulum Ya Karɓi Bakuncin Sarakunan Arewa a Maiduguri

Rashin Tsaro: Zulum Ya Karɓi Bakuncin Sarakunan Arewa a Maiduguri

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya karɓi bakuncin taron kwamitin zartarwa na 7 na Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa a ranar Talata, a birnin Maiduguri, babban birnin jihar. Taron ya mayar da hankali kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a yankin Arewa.

Taron, wanda taken sa shine “Ƙarfafa Tsaro a Matsayin Hanya Mafi Inganci Don Samun Daidaito da Ci Gaban Arewa,” an buɗe shi ne da sunan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, wanda Gwamna Zulum ya wakilta.

A jawabin sa, Gwamna Zulum ya bayyana cewa tsaro da zaman lafiya, noma da ƙarfafa matasa su ne ginshiƙan ci gaban da za a iya dogaro da su a yankin Arewa.

Ya ce, “Yawan matasanmu na da yawa kuma suna da kuzari, amma babu dama. Wannan gibi yana da hadari. Dole ne mu zuba jari sosai a fannin koyon sana’o’i, ilimin fasaha, kirkire-kirkire da kuma kasuwanci. Idan an ba matasa dama, ba za su fada cikin laifi ko tsatsauran ra’ayi ba, za su zama ginshiƙai na ci gaba.”

Zulum ya ƙara da cewa noma shi ne gindin tattalin arzikin Arewa, amma matsalar tsaro ta hana manoma ci gaba da ayyukansu a karkara.

Ya ce, “Muna da filayen noma masu yawa da jama’a da suka saba da aikin gona. Amma matsalar tsaro ta hana noma. Dole ne mu tabbatar da tsaron filayen noma da kuma tallafa wa noma ta zamani don dawo da rayuwa da rage dogaro.”

Ya ci gaba da cewa: “A madadin gwamnatin Jihar Borno da al’ummar ta, ina tabbatar muku da kudirin mu na samar da zaman lafiya, adalci da ci gaba tare. Tare da ƙwazo da haɗin kai, za mu sake gina Arewa ta fuskar jiki, zamantakewa da tattalin arziki.”

Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Arewa kuma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bayyana cewa an gudanar da taron a Borno ne domin ƙarfafa haɗin kai da kuma tattauna matsalolin yankin don bai wa shugabannin siyasa goyon baya wajen magance su.

An samu wakilcin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro, Babban Hafsan Tsaro, da Sufeto Janar na ƴan sanda.

Sauran da suka halarta sun haɗa da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, wanda Mataimakinsa, Manassah Daniel Jatau, ya wakilta, Sanata Kaka Shehu Lawan, Shehun Borno, Abubakar Ibn Garbai Umar, da sauran sarakuna daga jihohi 19 na Arewa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments