Da misalin ƙarfe 2:30 na safiyar yau, Gwamna Dikko Umaru Radda yana duba shafukan sada zumunta ne sai ya ci karo da wani gaggawan sakon Facebook da ke nuni da wata gobara da ta tashi a Sabon Titin Kwado. Babu wata ɓata lokaci.

“Na ga sakon ne yayin da nake yawo a shafin Facebook, inda al’umma ke neman agaji. A lokacin nan na fahimci cewa ba zan tsaya watsar da bayanin kawai ba. Mutanena ne ke cikin haɗari,” in ji Gwamna Radda.
Wanda ya wallafa sakon a Facebook ya ce tuni ya sanar da ma’aikatan kashe gobara, amma suka ce suna da matsalar fasaha da ya hana su isa wurin. Wannan ya sa Gwamna Radda da kansa ya wuce ofishin kashe gobara, ya jagoranci tawagar da za ta je wajen gobarar – babu jiran rahoto, babu tura wakili – kai tsaye ya tashi don ceton rayuka.

Da isarsa Sabon Titin Kwado, Gwamna Radda ya shiga aiki tare da ma’aikatan kashe gobara, yana tsara yadda za a shawo kan gobarar da kuma kwantar da hankalin wadanda lamarin ya shafa har sai da gobarar ta dauke baki daya.
Al’ummar da ke wajen sun bayyana mamaki da godiya ganin Gwamna da kansa cikin wannan mawuyacin hali.

“Wannan shi ne shugabanci na gaskiya. Ba wai ya aika mutane kawai ba – ya zo da kansa,” in ji wani mazaunin unguwar.
Dawowar Gwamna Radda cikin gaggawa da shiga cikin al’amarin da kansa a daren yau, na nuna irin yadda yake da niyyar kasancewa kusa da jama’ar Katsina a kowane lokaci da yanayi.

Gaskiya, shugabanci ba wai bin dokoki da tsari kawai ba ne – sai an kasance a shirye don tsayawa tare da jama’a a lokacin da suka fi bukata. Wannan shi ne Dikko Radda – Gwamna mai cike da tausayi.
Ibrahim Kaula Mohammed
Shugaban Ma’aikatan Yada Labarai na Gwamnan Katsina.


