Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya karbi rahoton karshe daga kwamitin rabon tallafin da ambaliyar ruwa ta shafa wadda tun tunin ya amince da fitar da zunzurutun kudi kimanin N18.08b da aka raba ga magidanta 101,330 da ambaliyar ruwan ta shafa.
Da yake bayar da cikakken bayani kan yadda kwamitin da gwamnan ya kafa don tantance asarar da aka yi da kuma gano ainihin mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa kai tsaye a dakin taro na gidan gwamnatin da ke Maiduguri, shugaban kwamitin injiniya Baba Bukar Gujibawu ya bayyana cewa an raba tsabar kudi naira biliyan 18.08 ga magidantan da suka rasa matsugunansu tare da abinci da sauran su.
A cewarsa an kuma an samu gudunmawar da ta kai naira biliyan 4.3 daga hukumomin kasa da kasa da suka hada da UNHCR, WFP, FAO, UNDP da sauran abokan hulda sun taimaka wajen bukatun gaggawa da aka bukata.
Gujibawu ya jaddada cewa sama da mutane miliyan daya ne ambaliyar ta shafa, in da magidanta 101,330 suka rasa matsugunansu.
Ambaliyar ta kuma haifar da lalata kayayyakin more rayuwa da filayen noma da kuma asarar rayukan mutane masu yawan gaske.
Ya ce kwamitin ya samu jimillar naira biliyan 28.2 ta hanyar asusun karo-karo da suka kunshi gwamnatin tarayya da na Jihohi da kungiyoyi da kuma daidaikun jama’a da suka tallafa.
Wannan ya hada da gagarumin gudunmawar naira biliyan 10 daga gwamnatin jihar Borno.
Bugu da kari, kwamitin ya samu gudunmawar magunguna, kayayyakin jinya, abinci da sauran muhimman abubuwan da suka kai biliyoyin naira.
“Kwamitin ya kuma ware naira miliyan 987 don taimakawa ‘yan kasuwa 7,716 a kasuwannin da abin ya shafa, ₦313 miliyan zuwa wuraren ibada 814 sai naira miliyan 213 ga makarantu masu zaman kansu kimanin 267 sai naira miliyan 89.4 ga matasa 1,788 da suka bayar da gudumawa a lokacin ambaliyar, da kuma naira miliyan 125 ga asibitoci masu zaman kansu”, in ji Gujbawu.
Kwamitin ya ba da shawarar a yi amfani da ragowar naira biliyan 4.45 wajen gyara hanyoyi a yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa, ciki har da titin Gongulong da ke birnin na Maiduguri.
“Injiniya Gujbawu ya mika godiyarsa ga gwamna Babagana Zulum bisa rashin tsoma bakinsa a cikin aikin kwamitin, sannan ya yabawa mambobin kungiyar bisa jajircewa da suka yi har kaiwa ga karshen aikin wannan kwamitin na su.”
Da yake mayar da martani, Gwamna Zulum ya ba kwamitin tabbacin aiwatar da dukkan shawarwarin da aka gabatar, inda ya ba da umarnin a gaggauta samar da tsarin tunkarar bala’i na dindindin a hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar (SEMA).
Zulum ya kuma umurci sakataren gwamnatin jihar da ya samar da hanyoyin da za a bi domin samar da sunayen tituna da lambobin gidaje yadda ya kamata a dukkan al’ummomin da ke cikin babban birnin jihar da kewaye.
Gwamnan ya kuma umurci ma’aikatar ayyuka da ta gaggauta sake gina hanyoyin sadarwa da ambaliyar ruwa ta lalata a garuruwa daban-daban da ke Jihar.
Zulum ya yabawa gwamnatin tarayya bisa gagarumin tallafin da take baiwa wadanda bala’in ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri.
Ya kuma mika godiyarsa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa yadda ya taimakawa al’ummar Borno a lokacin bala’in ambaliyar ruwan.
Gwamnan ya kuma yabawa kwamatin bisa gagarumin aikin da yake yi: “Bari in yabawa mambobin wannan muhimmin kwamiti bisa ga kwazon da kuke yi.” “In sha Allahu ‘yan baya za su yi muku addu’a mai kyau yayin da suka tadda tarihin wannan gagarumin aikin da kuka yi.”


