Daga, Sani Gazas Chinade , Damaturu
A ranar kirsimeti ne dai Kwamandan runduna ta 2 ta hadin gwiwa ta shiyyar Arewa maso Gabas Operation HADIN KAI, Maj-Janar MCE Ejike, ya shirya liyafar cin abincin Kirsimeti ga dakarun da ke gaba na rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai a Buni-Gari.
Da yake jawabi a wurin liyafar cin abincin Kirsimeti, Kwamanda sashi na 2, ya ce cin abincin Kirsimeti wata hanya ce da jami’ai da mazan da ke kan gaba za su taru domin nishadi tare da inganta zumunci.
Ya bayyana cewa irin wannan abin yabawa ne wanda ya samo asali daga kyawawan halaye na shugabancin Hafsan Sojan kasa Lafyanal Janar OO Oluyede NAM (COAS) da nufin zaburar da sojoji da kuma kara sada zumunci a tsakanin jami’an na ta.
Ya kuma yabawa babban hafsan tsaro (COAS) bisa irin goyon bayan da yake baiwa taron musamman da kuma jajircewarsa na inganta kwarewa da tsarin tafiyar da rundunar sojin Najeriya.
“Ya kuma sake nanata cewa “tushen ayyukanmu ya dogara ne kan Falsafa na rundunar babban hafsan tsaron wanda ke cewa, ‘Don karfafa sauye-sauyen sojojin Najeriya zuwa kwazo da kuma shirye-shiryen rundunar alhakin kundin tsarin mulki ne”.
A nasa jawabin, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni wadda kwamishinan ma’aikatar samar da arziki da aikin yi Aji Yerima Bularafa ya wakilta, ya ce tabbas sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara a yakin da ake yi da ‘yan tada kayar baya.
Buni ya bayyana cewa matsalar tsaro ta inganta sosai a jihar fiye da yadda ake tsammanii.
Ya ce jihar na daya daga cikin mafi zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya a halin da ake ciki.
“Ya kuma bada tabbacin Gwamnatin jihar Yobe za ta ci gaba da tallafa wa sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro a iyakar abin da ta ke da shi.
“Gwamnatin jihar za ta cigaba da bayar da tallafi ta fannin kiwon lafiya da kayayyakin masarufi, motoci, da gyaran kayan aiki da sauran nau’o’in kayan aiki da tallafi ga rundunar da aka tura jihar.” Inji shi.


