Saturday, June 13, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamna Radda Ya Nada Sabon Shugaban Ma'aikatan Gidan Gwamnati Da Wasu Mukamai 

Gwamna Radda Ya Nada Sabon Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati Da Wasu Mukamai 

Gwamnan ya amince da nadin tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya, Hon. Abdulkadir Mamman Nasir a matsayi shugaban ma’aikatan a fadar gwamnatin jihar. Abdulkadir Mamman Nasir, ya samu takardar shaidar kammala karatun digiri a jami’ar Bayero ta Kano. Ya rike mukami na, Babban Dirakta a Hukumar Raya Ruwa ta Jihar Katsina.

Abdulkadir Nasir zai maye gurbin tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jiha Hon. Jabiru Abdullahi Tsauri, wanda aka nada a matsayin mai kula da sabuwar kawance don ci gaban Afirka (NEPAD) na kasa.

Hakazalika, an nada Alhaji Malik Anas a matsayin Kwamishina, idan har majalisar dokokin jihar ta tabbatar da hakan. Alhaji Anas ya yi digirinsa na biyu a fannin kasuwanci a Jami’ar Bayero ta Kano. Haka nan kuma ya taba zama Babban Akanta Janar na Jihar Katsina, kuma memba a kungiyoyi daban-daban. Anas, har zuwa sabon nadin nasa shi ne mai ba gwamnan jihar Katsina shawara na musamman kan harkokin banki da kudi.

Gwamnan ya kuma amince da nadin Alhaji Mustapha Bala Batsari a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan bunkasa kasuwa. Bala ya yi Difloma mai zurfi a fannin harkokin gwamnati daga Makarantar kimiyya da fasaha ta jihar Kano. Ya rike mukamin Shugaban Hukumar Kare Muhalli ta Jihar (SEPA).

A daya bangaren kuma an nada Alhaji Nasiru Ahmed a matsayin mai ba da shawara na musamman kan raya karkara da zamantakewa.

Hajiya Bilikisu Suleiman a matsayin mai ba da shawara ta musamman kan harkokin banki da kudi. Bilikisu ta kasance Babban Sakatariya ta Hukumar Kula da Ci Gaban Jihar Katsina har zuwa sabon nadin nata.

Abubakar Ahmad Tsanni a matsayin mai ba da shawara na musamman kan ci gaban matasa, ya taba zama mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin wasanni da ci gaban al’umma.

Dr. Mustapha Shehu zai yi aiki a matsayin Babban Sakataren Hukumar Kula da Ci Gaban Jihar Katsina (KSDMB). Shehu wanda ya samu digirin digirgir a fannin Fasahar kirkira daga Jami’ar De Sonora ta kasar Mexico,

Engr. Aminu Barau Mairuwa, wanda aka nada a matsayin babban mataimaki na musamman (SSA) ga gwamna kan sabon tsarin cigaban al’umma (CDP),  Har zuwa lokacin da aka nada shi, ya kasance Babban Manaja na Hukumar Kula da Gidaje ta Jihar Katsina.

Hakazalika, Dr. Aliyu Rabi’u Kurfi zai karbi ragamar hukumar kula da gidaje ta jihar Katsina a matsayin babban Manaja,  Har zuwa nadin nasa, Kurfi ya kasance Babban Director a Ofishin Tarihi da Al’adu na Jihar Katsina.

Bugu da kari, an nada Dr. Kabir Ali Masanawa Babban Director Hukumar Tarihi da Al’adu ta Jihar Katsina.

Zuwaira ibrahim Boyi ta maye gurbin Dr. Kabir Masanawa a hukumar kula da cigaban jihar Katsina, An nada Alhaji Abdullahi Abubakar Gagare.

DAGA. Ibrahim Kaula Mohammed
Babban Sakataren Yada Labarai Gwamnan Jihar Katsina

*Fassarawa*
*Abubakar Balarabe Turaki*

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments