Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da wani taro da nufin gyara tsarin ilimin Almajiranci, tsarin koyar da addinin Musulunci na gargajiya da ya zama ruwan dare a arewacin Najeriya.
Taron wanda aka gudanar a dakin taro na Sakatariyar Musa Usman da ke Maiduguri na neman kawar da mummunar tafsirin ilimin addinin musulunci da ya taimaka wajen bullowar mayakan Boko Haram.
Zulum ya bayyana cewa manufar taron shine magance matsalolin rashin tsaro ta hanyar ilimi ga daukacin ‘yan Borno.
“Don ganin an cimma hakan, gwamnatin jihar Borno ta kafa hukumar kula da ilimin larabci da tsangaya, inda ta bullo da tsarin karatun bai daya na makarantun tsangaya da na Islamiyya.
“A cewar sa wannan tsari ya hada da manyan kwalejojin Islama da ke kula da yara almajirai da ya hada manhajoji na addini da na boko wuri guda.”
“Sake fasalin tsangaya zai baiwa almajiri kyakkyawar dama a rayuwa kasancewar manufar gwamnati ita ce daidaita tsarin ilimi na yau da kullun zuwa ingantattun makarantun tsangaya don shiga kwaleji da jami’a,” in ji Zulum.
A jawabinsa shugaban hukumar Ilimin Larabci da tsangaya ta Jihar Borno, Sheikh Arabi Abulfatahi, ya gode wa Gwamna Zulum bisa tallafin da ya bayar.
Baki da suka gabatar da jawabi sun hada da Farfesa Mustapha Gwadabe da Mohammed Alhaji, yadda suka bukaci a yi wa tsarin almajiri garambawul.
Taron ya tattaro masu ruwa da tsaki a harkar ilimi, da malaman addini, da masu fafutukar kare hakkin al’umma, domin tattaunawa kan hade almajiranci da ilimin boko.


