Daga Sani Gazas Chinade, Maiduguri
Hukumar raya yankin arewa maso gabas, NEDC, ta kwashe magudanar ruwa mai tsawon mita 300,000 a cikin birnin Maiduguri na jihar Borno don magance ambaliyar ruwa da al’ummar birnin ke fama da shi a duk lokacin damina.
Magudanar ruwan da aka kwashe suna cikin unguwannin Bulumkutu, Gwange, da Fezzan, da Kuma yankin rukunin gidajen gwamnati (GRA) da ke babban birni.
Da yake bayyana matakan dakile matsalar ambaliyar ruwa a Maiduguri, Manajan Darakta na Hukumar NEDC, Mohammed Alkali, ya bayyana cewa: “Mun yi niyya wajen yashe magudanan ruwa na kimanin mita miliyan daya a cikin manyan biranen jihohi shida na yankin Arewa maso Gabas.
Bayan kwashe magudanun ruwa, ya kara da cewa, sharar da aka tattara da sauran sharar da ake samu daga al’umma za a sake yin amfani da su tare da sarrafa su don zama dukiya.
Alkali ya lura da cewa ci gaba da kwashe sharar da matasa ke yi don samarwa kan su kudaden shiga ba wai kawai zai rage datti bane a Maiduguri ba har ma zai tabbatar da tsafta a al’ummomin da abin ya shafa.
Dangane da illar lafiyar matasan, ya ce, “matasan da ake magana akan su da ke hawa kan bola ko Kuma juji an ba wa kowannensu takalman aiki, safar hannu, da kuma abin rufe fuska,” yana mai cewa wadannan kayayyakin aiki za su hana su kamuwa da kowace cuta kamar kwalara da sauran cututtukan da ke haifar da ruwa. .
Da yake magana kan hanyoyin da za a bi wajen magance ambaliyar ruwa na tsawon lokaci, ya ce an dauki wani kwararren jami’in kan harkokin kiwon lafiya don samar da cikakkiyar mafita ga matsalar ambaliyar ruwa a Bulumkutu.
Ya yi nuni da cewa babban jami’in zai gina magudanar ruwa mai fadin mita wanda zai iya kwashe ruwan da ke cikin kogin Ngadda da makamancin haka.