Daga, Sani Gazas Chinade, Maiduguri
Gwamnatin jihar Borno ta jaddada kudirinta na magance kwararowar yaran da ba su da Jagora daga shigowa babban Birnin jihar Maiduguri da zimmar neman kudi wadda a mafi yawan lokaci suke haifar da barazana ga zaman lafiyar al’umma.
Kwamishinan yada labarai da tsaron cikin gida, Farfesa Usman Tar ne ya bayyana haka bayan taron majalisar tsaro na jihar da aka gudanar karkashin jagorancin Gwamna Zulum a gidan gwamnatin da ke Maiduguri.
Kwamishinan ya ce, “Majalisar ta yi zamanta ne domin duba yanayin tsaro a jihar bayan yin nazari sosai kan duk abin da ya faru daga ranar 1 zuwa yanzu, majalisar ta cimma matsayar hakan.”
Ya kara da cewa, daga cikin kudurorin da aka cimma, kwamitin tsaro ya amince da cewa, za a rika sa ido da kuma kula da jigilar yaran da ba su Jagora na gari zuwa Maiduguri daga yanzu.
Ya Kara da cewa, yaran da aka gano suna da kulawar iyaye ne kawai za a bar su su shiga babban birnin jihar.
Kwamishinan ya kuma cigaba da cewa gwamnatin jihar Borno ta sha alwashin ci gaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na tabbatar da doka da oda a Borno.
Ya kuma ce wani bangare na kudurin majalisar shi ne tabbatar da cewa an gaggauta gurfanar da wadanda aka kama gaban kuliya.
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa, za a bi shari’ar kananan yara yadda ya kamata, kuma an ba wa ma’aikatar shari’a umarnin samar da tsarin shari’ar kananan yara nan take.
Ya bukaci jama’a da su tallafa wa jami’an tsaro da bayanan sirri na asali domin su taimaka wajen wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Borno.


