Saturday, June 13, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiGwamna Zuum Ya Sake Tsugunar Da Al'umomi 10 Da Suka Rasa Matsugunansu...

Gwamna Zuum Ya Sake Tsugunar Da Al’umomi 10 Da Suka Rasa Matsugunansu A Borno

Daga Sani Gazas Chinade, Maiduguri

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da gidaje 500 a Nguro-Soye, karamar hukumar Bama, domin sake tsugunar da al’ummomi 10 da rikicin ‘yan tada kayar baya da aka kwashe shekaru sama da goma ana yi ya raba su da matsuggunnan.

Shirin sake tsugunar da matsugunan, wanda zai amfanar da magidante sama da 1,100, ya kunshi wuraren bukatun jama’a na rayuwa da suka hada da makarantu, cibiyoyin kiwon lafiya, cibiyoyin samar da ruwan sha, da sauran ababen more rayuwa.

Gwamna Zulum, a lokacin kaddamar da aikin, ya jaddada kudirinsa na sake gina Borno da kuma rufe dukkanin sansanonin ‘yan gudun hijira nan da shekarar 2026 In Allah ya so.

Ya kara da cewa ayyukan sake gina garin Bama bai tsaya ga garin na Bama kawai na har ma da wasu garuruwan da suka hada da garuruwan Banki, Nguro Soye, da Mallam Chelumri, da kuma kokarin da ake yi a Garin Tarmua, Kumshe, Mayanti, da Bula Yobe da nufin sake tsugunar da ‘yan gudun hijirar wadannan garuruwa da zimmar  sake gina hadaddiyar Borno.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments