Daga Muhamnad Sani Chinade, Damaturu
Wasu Al’ummomin jihar Yobe sun bayyana jin dadinsu tare da yabawa Gwamna Mai Mala Buni kan gina hanyoyin mota a yankunan su da ma dukannin sassan jihar.
Mazauna wasu ssssan Jihar sun yi wannan yabon ne a wata hira da suka yi da manema labarai yayin wani rangadin da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Yobe ta shirya.
Malam Kadu Kafayo, wani mazaunin garin Tagali a karamar hukumar Bade ya ce hanyar Chumbusko zuwa Tagali mai tsawon kilomita 10 ta kawo musu saukin rayuwa matuka
“Kafin samar da hanyar, da kyar muka iya kai amfanin gonakinmu zuwa kasuwanni daban-daban a ciki da wajen jihar Amma saboda Gina mana wannan hanyar mota ga shi “Yanzu mun yi farin cikin kasancewa tare da sauran sassan jihar,” in ji shi.
Malam Sama’ila Tagali, wani direban mota ya yabawa gwamnan tare da yin kira da a samar da wuraren ajiya domin adana amfanin gonakinsu.
Alhaji Muhammadu Chukuriwa Hakimin Kauyen Chukuriwa shi ma yabawa ya yi ga Gwamna Buni akan titin Dawasa, Chukuriwa, Kukuri mai tsawon kilomita 16.5 da aka Gina Musu.
Ya ce hanyar ta hade kauyuka da dama da ke kan hanyar da babban garin Potiskum.
Ya kuma yabawa gwamna da kwamishinan ayyuka Alhaji Umar Wakil Duddaye kan aikin gina masallacin Juma’a na garin Chukuriwa.
Shi ma Malam Ishaku Ado, Masaya na Kukuri ya nuna jin dadinsa kan wannan aiki.
Ya kara da cewa al’ummar yankunan uku za su ci gaba da godiya ga Kwamishinan Ayyuka, wanda shi ne ya gudanar da aikin.
A garin Fika, mataimakin shugaban karamar hukumar ya ce, wannan na daya daga cikin aikin da daukacin al’ummar wannan karamar hukumar za su amfana.
Domin an shafe shekaru da dama kafin a tabbatar da shi, shi ya sa ya zama mai cike tarihi abin yabo ga wannan gwamnati.
Ya kara da cewa aikin ya hada kusan unguwanni biyar da kananan hukumomi uku na Fika, Gujba da Gulani.
A nasa jawabin, shugaban kungiyar ta NUJ, Rajab Muhammed Ismail ya bayyana jin dadin ayyukan da aka gudanar tare da yabawa Gwamna Mai Mala Buni bisa ga kwazonsa.
Ya yi kira ga sauran gwamnonin da su yi koyi da gwamna Buni domin ci gaban jihohin su.


