Monday, April 28, 2025
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabarai‘Yan Daba Sun Tarwatsa Masu Zanga-zanga A Legas 

‘Yan Daba Sun Tarwatsa Masu Zanga-zanga A Legas 

Wasu ‘yan daba sun tarwatsa wasu masu zanga-zangar nuna adawa da kunci da yunwa a jihar Legas a ranar Litinin, yayin da suka taru a sakatariyar Alausa da ke Ikeja.

‘Yan daban sun iso wurin ne a cikin wata motar bas ta damfo mai launin rawaya inda suka fatattaki masu zanga-zangar da suka taru, sannan suka kwashe allunan rubuce-rubucen kokensu.

Jami’an rundunar ‘yansandan Nijeriya da ke daura da sakatariyar Alausa tun da farko sun hana masu zanga-zangar a lokacin da suke rera wakokin zanga-zangar tare da yin kira ga gwamnati da ta saurari bukatarsu.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ‘yansandan da ke wurin ba su hana ‘yan daban tarwatsa masu zanga-zangar ba.

Leadership Hausa

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments