A halin yanzu shugaba Bola Tinubu na wata ganawar sirri da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da wasu gwamnoni a ofishinsa da ke fadar gwamnatin tarayya a ranar Alhamis.
An fara ganawar ne bayan da shugaban ya kammala tattaunawa da shugabannin kungiyar kwadagon, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi sabon tsarin mafi karancin albashin ma’aikata.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF), AbdulRahman AbdulRazaq na Jihar Kwara; Charles Soludo na Jihar Anambra da Usman Ododo na Jihar Kogi.
Ya zuwa yanzu dai ba a san makasudin taron ba, amma yana zuwa ne sa’o’i kadan bayan da kotun kolin ta yanke hukunci kan bai wa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai.
Leadership Hausa