Saturday, June 13, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiWani Sabon Mahadi Ya Bayyana A Kaduna

Wani Sabon Mahadi Ya Bayyana A Kaduna

Daga Imrana Abdullahi

AbdulRahman Muhammadu Bello Kuso, wani matashi ne mai da’awar addinin Islama da ya yi kira ga mabiyan addinin Musulunci da Kirista da kowa ya yi hattara da zamanin da muke ciki na karshen zamani domin duniyar ta zo karshe.

AbdulRahman Muhammad Bello Kuso, ya ce idan mutum ya kula sosai da idanun basira wannan duniyar ta zo karshe domin za ta kare

Muhammad Kuso, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a cikin dakin taro na cibiyar yan jarida ta kasa NUJ da ke Kaduna.

Kuso, ya ce shi mutumin garin Lafai ne ta Jihar Neja kuma Babansa ya je garin Yan Tumaki a Jihar Katsina don haka shi jikan Daudu Maza ne saboda haka shi ba boyayye ba ne a Najeriya.

Sai ya yi kira ga dukkan al’umma da su hanzarta samar da hanyoyin zaman lafiya domin kawo karshen irin zubar da jinin da ake yi na kashe – kashe a fadin Najeriya.

Ya kara da cewa shi ne sabon Mahadin da ake jiran zuwan sa kuma ya na da cikakkun hujjojin da zai iya kalubalantar duk wani mai yin inkarin hakan.

“Ina zaune ne a garin Kaduna kuma a shirye nake domin gabatar da mubahala da duk wani da ke inkarin magana da Da’awar da nake yi domin ceton al’ummar Kirista da Musulmi, littafin da nake da shi a yanzu a wuri na ya na dauke da komai da komai don haka akwai Isassun hujjoji a tare da Ni”, inji Bello Kuso.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments