Wakilinmu Bashar Isah Daura ya halarci fadar mai martaba Sarkin Daura, inda ya hada mana rahoto kan yadda hakimai da dagatai daga sassa daban-daban na masarautar Daura suka gudanar da gaisuwar Jahi/Jafi ga mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq Umar, a ranar Talata 26 ga watan Mayun 2026, a jajibirin babbar Sallah ta layya.
An gudanar da taron ne a fadar mai martaba Sarkin da ke Daura, inda dubban jama’a suka hallara domin shaida wannan al’ada ta gargajiya da ke nuna biyayya da girmamawa ga masarauta.
Taron ya samu halartar hakimai da dagatai daga sassa daban-daban na masarautar Daura, tare da baki daga ciki da wajen jihar Katsina da ma wasu sassan Najeriya.
A yayin gudanar da gaisuwar, mahalarta taron sun bayyana farin cikinsu bisa yadda masarautar Daura ke ci gaba da raya al’adun gargajiya da suka gada tun kaka da kakanni, musamman a irin wannan lokaci na bukukuwan Sallah.
Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq Umar, ya yaba da irin hadin kai da biyayya da hakimai da dagatai ke nunawa masarautar, tare da yin addu’ar samun zaman lafiya da ci gaba a masarautar Daura da kasa baki daya.
Daga cikin wadanda suka bayar da gudunmawa da taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da taron akwai Dakamawa, Sarkin Wakan Sarkin Daura, Wakilin Sarkin Busa da sauran masu ruwa da tsaki a masarautar.


