Saturday, April 18, 2026
spot_imgspot_imgspot_imgspot_img

Katsina state government

HomeLabaraiBala Wunti: Zaren Ɗinke Ɓarakar Siyasa a Jihar Bauchi

Bala Wunti: Zaren Ɗinke Ɓarakar Siyasa a Jihar Bauchi

Usman Abdullahi Koli

A lokacin da mutane da dama ke cike da fargabar rikicin cikin gida da ka iya ɓarkewa ya kuma haifar da rarrabuwar kai a tsakanin manyan ‘yan siyasar jihar Bauchi, lokacin ne da ake sauya fasalin siyasa a matakin ƙasa da jihohi, sai ga wani mutum da ya zo da manufar haɗa kan jama’a da samar da hanya mai ɓullewa, musamman bayan zaɓukan da suka gabata.

Yanayin siyasa, musamman na Jihar Bauchi, ya saba da rikice-rikice da nuna son zuciya daga wasu tsirarun masu ruwa da tsaki. Yayin da jihar ke fuskantar ƙalubale da dama da ke buƙatar gyara cikin gaggawa da ƙwarewa, tambayar ita ce: wa zai iya cimma waɗannan kyawawan manufofi? A nan ne ya kamata mu duba dacewar Bala Wunti a wannan lokaci mai sarƙaƙiya.

Daga cikin ‘yan siyasa da suka fito zawarcin kujerar gwamnan Bauchi a kakar zaɓen bana, babban abin da ya kamata a duba shine haɗin kai bisa kyakkyawar manufar ceto al’ummar jihar, a fitar da tsarin yaƙar talauci, rashin tsaro, yunwa, rashin aikin yi, da sauran matsalolin da ke hana mu ci gaba da gogayya da sauran jihohin da suka yi mana fintinkau.

Akwai wasu mutane da shigar su siyasa na iya kawo mafitar da ma hukumomi suka gaza samarwa tsawon lokaci. Halayensu kuma na sa har masu kallonsu cike da shakku su yarda cewa har yanzu nagarta na da muhimmanci musamman ga jagororin jama’a. Dr. Bala Maijama’a Wunti na daga cikin irin waɗannan mutane. Labarinsa ba na tashen dare ɗaya ba ne, labari ne na yadda rayuwa ta ginu bisa ƙalubale, faɗi-tashi da jajircewa duk rintsi, kuma aka ɗora ta bisa ginshiƙin gaskiya, jin ƙai da kishin al’umma tun farko.

Fitowarsa daga tsatson masu ƙaramin ƙarfi ya sa rayuwa ba ta hannanta masa damammaki cikin sauƙi ba, hasali ma dai, tun wuri ta yi tsananin da ta tilasta masa zama mai juriya, ya kuma koyi dogaro da kai. Kowane mataki na rayuwarsa cike yake da rashin tabbas, sai dai hakan bai sa ya zama mugu, ko wanda zuciyarsa ke cike da ƙunci da kyashi ba, sai ya koyi haƙuri, tausayi, da nutsuwa yayin da al’amura suka rincaɓe. Inda wasu kan gigice, yakan tsaya cike da nutsuwa. Wannan wata kyakkyawar ɗabi’a ce da ake buƙatar shugabanni da ita.

*Tarihin Rayuwa da Aiki*

Neman ilimi da Bala Maijama’a Wunti ya bi irin tafarkin da rayuwarsa ta faro a kai, zango ne na jajircewa da fuskantar ƙalubale. Daga karatun Chemistry a Jami’ar Ahmadu Bello, zuwa samun horo a fannin gudanarwa a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ƙarin kwasa-kwasai a wurare da dama, kowane mataki alama ce ta sadaukarwa. Abin da wannan gwagwarmaya ta samar ba mutum mai ilimi ba ne kaɗai, ta samar da mutum mai fahimta, wanda ya san sarƙaƙiyar al’amura, yake mutunta tsarin gudanarwa, kuma yake girmama hangen nesa. A duniyar da ake gaggawa, ya zaɓi bin doguwar hanyar cimma nagarta, wannan kuma ya shafi kowane ɓangare na rayuwa da aikinsa.

Lokacin da ya fara aiki da Kamfanin Mai na Ƙasa wato NNPC Limited a 1994, ya tsinci kansa a ɗaya daga cikin ma’aikatu mafi tsauri a ƙasar nan. Duk wani alheri da ke tattare da sunansa a yau, ba daga sama ya zo ba, Daga matsayinsa na farko na Production Programming Officer har zuwa Chief Upstream Investment Officer, tafiyarsa ta nuna ci gaba da ya wanzu bisa ƙwarewa, ba surutu da bambaɗanci ba. Ya fahimci tsarin ciki da bai, ya gane matsalolinsa, kuma ya zaɓi kawo gyara, ba zama ɗan kallo kawai ba. Yayin da wasu ke neman suna, ya samar wa kansa gurbin zama bisa ƙwarewa. Yayin da wasu suka bazama neman muƙamai da sarautu, shi ya tsaya domin samun gogewa a fagen jagoranci da warware matsaloli.

Nauyin gudummuwar da ya bayar a fannin mai da iskar gas a bayyane yake a ma’auni na zahiri a idon masu bibiyar al’amura. Ya taka rawar gani wajen ƙarfafa tsarin zuba jari, dawo da tsarin aiki bisa kwarewa, da gyara ayyukan da suka daɗe suna gudana ba tare da tabbataccen tsari ba. Shirye-shirye da ya aiwatar irin su Operation White ba garambuwal ga fannin aiki da fasahar zamani kawai suka yi ba, sun kuma nuna cewa ana iya samun gaskiya da riƙon amana ko da a wurare masu rikitarwa. A wannan wuri da kowace shawara ke tasiri ga rayuwar duk wani ɗan ƙasa, salon gudanar da aikin sa ya kasance cikin natsuwa da hangen nesa, ya fifita ribar da za ta mamaye ko’ina a tafiya mai dogon zango, saɓanin masu azarɓaɓin da kan nemi yabo cikin ƙanƙanin lokaci. Wannan shi ne bambanci tsakanin masu tafiyar da tsarin da suka tarar da masu ƙarfin hali da ilimin sauya shi zuwa tsari mafi kyau, mai ɗorewa.

Taƙaita rayuwarsa ga nasarorinsa a aikin gwamnati kaɗai tamkar cin tuwo ne babu miya. Abin da ya bambanta Bala Wunti da sauran mutane ba wai abin da ya yi a ma’aikatun gwamnati ba ne, har da abin da ya yi a wajen su, wanda kuma wannan shi ne ɓangaren da al’ummarsa ta fi tasirantuwa da nasararsa. Hausawa na cewa ɗan halas ba ya manta mafari, don haka Bala Wunti bai manta wahalhalun da ya sha a rayuwa ba, sun zamar masa fitila wajen haska buƙatun al’umma, tare da ba shi ƙaimin ƙoƙarin magance damuwarsu. Sanin inda ya fito, da yadda ya taso yana tasiri kan yadda yake mu’amalantar mutane, da kuma yadda yake jajircewa wajen tallafa wa mabuƙata gabas da yamma, kudu da arewa. Ba kuma tallafin wucin-gadi yake bayarwa ba, taimakon mabuƙata wani ɓangare ne na rayuwarsa ta yau da kullum. Ɗalibai da dama sun amfana, al’umma sun samu ci gaba, mabuƙata na samun taimako, kuma duk cikin sirri da mutuntawa ba tare da hayaniya ko gori ba. Tallafin da ya bayar ga ɗaliban makarantun gaba da sakandare ba tallafi falle ɗaya ba ne, a’a, al’adarsa ce. Wasu mutanen suna bayarwa a lokacin da bayarwa ke da sauƙi. Shi yana bayarwa ne saboda yana ganin hakan wajibi ne, domin tallafar al’ummarsa.

Sannan ɗabi’unsa ma ababen koyi ne, musamman ga matasa. Ba ya shiga sharo ba shanu. Ba ya sayar da ‘yancinsa don ribar rana ɗaya, yana ganin hakan a matsayin cin dare ɗaya. A yankin da a tsarin siyasa da aiki inda ake ɗaukar sassaucin ra’ayi a matsayin hikima saboda ba a san inda rana za ta faɗi ba, irin tsayuwar daka da yake yi kan abin da ya yi amanna da shi wani nau’i ne na jarumta, ta yadda duk wanda ya bi shi, yana da yaƙinin cewa yana biye da jagora kaifi ɗaya. Addininsa, wanda shi ne jigon rayuwarsa, yana ƙarfafar wannan jajircewa. Tsoron Ubangijinsa na bayyana a aikace, ba a baki kawai ba.

Lokacin da ya bar aikin gwamnati a ranar 30 ga Mayu, 2025, ya yi hakan a sirrance. Ba hayaniya, babu sharholiya. Wannan wata alama ce ta tabbacin mutum da ya san aikinsa na ƙwarai na wakiltarsa har a wuraren da ƙafarsa ba ta taka ba. Tasirinsa bai tsaya ga muƙami ba. Tsarabar da ya ɗauko ta ƙwarewa ce, riƙo da gaskiya da kuma amana. Waɗannan abubuwa sun fi ƙarfin kuɗi ya saya, sun kuma fi kowane mukami daraja.

Dole tattaunawar siyasa a Bauchi su canja salo. Jihar ta shallake matakin da za a yi ta maimaita dabaru da ayyukan baya da tunanin samun sabon sakamako. Ƙalubalen da muke fuskanta sun ƙaru, mutane sun zaƙu don ganin kawo sauyi, damar yin kuskure a mulki ta ƙara tsada. Wannan ba lokacin jin daɗi ba ne, lokaci ne na yanke shawara mai ma’ana. Dabarun siyasa kaɗai ba za su wadata ba, har da zurfin fahimta, ilimin tattalin arziki, da ikon juya buri zuwa sakamako.

A wannan gaɓar, yana da kyau mutanen Bauchi su tantance Bala Wunti, saboda yadda ya gudanar da rayuwarsa na alamta dacewarsa da angwancewa da jiharmu mai albarka. Yana da fahimtar tsarin mulki, ya gudanar da manyan ayyuka masu sarƙaƙiya cikin tsari da nasara. Yana da fahimtar jama’a da ta samo asali daga yadda ya taso, ba hasashe kawai ba. Abu mafi muhimmanci, ba ya cikin rikice-rikicen siyasa da suka daɗe suna addabar jihar. Wannan nisa da ya yi da surkullen siyasar ya tsaftace shi daga zargi da ɓatanci, haka kuma ya kare shi daga bayyana a matsayin wani ɓangare na waccan daɗaɗɗiyar hauma-haumar siyasa, ana ma iya cewa ya zama wata hanya ta ɗinke ɓaraka da haɗa kawunan masu mabambanta ra’ayin siyasa.

Gabatar da shi a matsayin mafi dacewa da kujerar gwamnan Bauchi ba ra’ayi ne da na gabatar bisa son zuciya ba, duk da dai labarin rayuwarsa yana taɓa zuciyar. Dalilin ganin dacewar sa yana da tushe mai wuyar ƙaryatawa. Tushen sa shi ne ƙwarewa, sanin makamar aiki, da tarihi da ke nuna sanin kai da jajircewa. A lokacin da amana ta yi ƙaranci, shigar sa siyasa ta zama kamar saukar ruwan sama ne bayan fari. A inda rarrabuwa kai ke raunana al’umma, kasancewarsa a tsakiya na iya kawo sauƙi. A lokacin da ake buƙatar ƙarfin ƙwanji, hangen nesa da kuma tausasawa, muna iya cewa ma kamar an yi Bala Maijama’a Wunti don ya zo a wannan lokacin ya ceci jiharmu ne.

Gabatar da shi a matsayin mafi dacewa ba ya nufin shi cikakke ne ko ya kore masa yiwuwar yin kuskure, duk ɗan’adam ajizi ne, kuma cikar kamala na ga Ubangiji. Sannan shugabanci ba ya tsayawa a buri kaɗai, ana ganinsa a yadda mutum ya gina rayuwarsa. Idan ana batun Bala Wunti, waɗannan hujjoji suna nan a fili. Daga tasowar sa cikin ƙalubale zuwa aiki mai matuƙar tasiri, muna iya cewa an riga an gwada shi, kuma an san na ƙwarai ne.

Bauchi na gab da yin zaɓi mai nauyi da tasirinsa ya fi zarce sanannun sunaye ko fastar zawarawanta. Zaɓi ne tsakanin nanata tsoffin hanyoyi da dabaru, da kuma yin garambawul ga tsarin gudanarwa da kawo sauyin da zai inganta rayuwar al’umma, zaɓi ne tsakanin abin da aka saba da abin da ake matuƙar buƙata. Idan mutanen jihar na son samun makoma mai cike da kwanciyar hankali, ƙwarewa, da ci gaba da zai karaɗe kowa da ko’ina, dole ne su gane wanda ya shirya samar da hakan idan sun gan shi.

Bala Wunti na da ƙwarewa, kyawawan halaye, da sanin makamar aiki. Ba sai ya faɗi ƙimarsa ba. Ayyukansa tabbatacciyar shaida ce ga nagatarsa. Tambayar ita ce: shin mutanen Bauchi sun shirya zaɓar irin mutumin da jihar ke matuƙar buƙata a wannan gaɓar?

Idan sun shirya, to amsar tana gabansu.

Usman Abdullahi Koli
mernoukoli@gmail.com.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments