Daga Aliyu Bala Gerengi a Gombe
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi kira ga al’ummar jihar da su kasance masu haƙuri, haɗin kai da zaman lafiya a harkokin shugabanci da siyasa.
Gwamnan ya kuma bukaci jama’a da su guji ƙiyayya, kalaman rarrabuwar kai da duk wani abu da ka iya haifar da tashin hankali a tsakanin al’umma.
Inuwa Yahaya ya yi wannan kiran ne a wajen rufe gasar haddar Alƙur’ani da karatunsa karo na 29, wadda Ƙungiyar Izala Assasawar Sheikh Ismaila Idris Jos ta shirya a garin Bambam, ƙaramar hukumar ci gaban Balanga ta Kudu a Jihar Gombe.
Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ne ya wakilci gwamnan a wajen taron.
Gwamna Yahaya ya yaba wa ƙungiyar bisa kokarin da take yi wajen tarbiyyantar da matasa ta fuskar addini da kuma bunƙasa karatun Alƙur’ani.
Ya tabbatar wa masu shirya gasar cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen da ke inganta ɗabi’u da tarbiyya, tare da samar da al’umma masu tsoron Allah da sanin nauyin da ke kansu.
Gwamnan ya kuma jaddada muhimmancin goyon bayan al’umma ga gwamnatinsa, yana mai cewa nasarorin da Jihar Gombe ta samu a shekarun baya sun samu ne sakamakon haɗin kai da goyon bayan jama’a.
Ya yi kira ga al’umma da su kasance masu natsuwa, tare da guje wa kalamai ko ayyukan da za su iya haddasa tashin hankali, kawo rabuwar kai ko barazana ga zaman lafiyar jihar.
Ya ce haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen ci gaba da ɗorewar ci gaban Jihar Gombe.
Gwamnan ya ƙara da cewa nasarorin da jihar ta samu sun jawo hankalin wasu jihohi, waɗanda ke ƙara nuna sha’awa ga tsarin ayyukan raya ƙasa da Gombe ta fara aiwatarwa.
Tun da farko, Shugaban Majalisar Ulama ta Ƙungiyar Izala, Sheikh Hamza Abdulhamid, ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da yi wa shugabanninsu addu’a tare da nuna haƙuri da juriya.
Malamin ya ce ƙungiyar Izala ta daɗe tana taka rawa wajen ilmantar da Musulmi, inda ta kafa makarantu a matakai daban-daban, tare da shirin kafa jami’a domin ci gaba da bunƙasa ilimin addini da na zamani.
Sheikh Hamza ya kuma yi gargadi kan kalaman rarrabuwar kai da rikice-rikicen da ba su da amfani, yana mai cewa bambancin ra’ayin siyasa bai kamata ya zama sanadin ƙiyayya ko gaba tsakanin ‘yan kasa ba.
Ya bukaci jama’a da su rungumi tattaunawa, haƙuri da zaman lafiya, yana mai cewa siyasa ya kamata ta zama hanyar warware bambance-bambance, ba kuma hanyar haifar da rikici ba.


