An samu rahoton cin zarafi daga wani jami’in hukumar Hisbah a jihar Katsina, inda ake zargin ya lakadawa wata matashiya mai suna Aisha Musa dukan kawo wuƙa ba tare da bin tsarin doka da oda ba.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8 na dare a ranar Talata, lokacin da Aisha ta ziyarci shelkwatar hukumar Hisbah da ke cikin birnin Katsina domin jin dalilin kama kaninta da hukumar ta yi.
Bayan fara tattaunawa da jami’in Hisbah ɗin mai suna Nafiu Kwamanda, rahotanni sun ce rikici ya shiga tsakaninsu, wanda daga bisani ya rikide zuwa cin zarafi inda ake zargin Kwamanda Nafiu ya daki Aisha Musa da ƙarfi har ta ji rauni.
Wakilinmu ya tuntubi shugaban hukumar Hisbah a jihar Katsina, Sheikh Abu Ammar, domin jin ta bakinsa game da lamarin, sai dai bai samu damar samun sa ba, kafin kammala hada wannan rahoto.
A gefe guda, mahaifiyar matashiyar ta bayyana damuwarta tare da neman a bi mata haƙƙin ‘ya’yanta, tana mai cewa: “Ba daidai bane a rika dukan mutane kamar dabbobi ba tare da gudanar da bincike da bin tsarin doka ba.”
Al’umma na ci gaba da bayyana damuwa kan yadda wasu daga cikin jami’an Hisbah ke aiwatar da ayyukansu cikin zalunci da nuna rashin da’a ga hakkokin ɗan Adam.
Za mu ci gaba da bibiyar wannan lamari domin kawo muku sabbin bayanai idan sun taso.