By Hussaini Ibrahim,Gusau
A ci gaba da gudanar da bukukuwan ranar ‘yan sanda ta kasa, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda CP Ibrahim Balarabe Maikaba, PSC, ta gudanar da gwajin lafiya kyauta a makarantar sakandiren Sambo da ke Gusau babban Birnin Jihar Zamfara a ranar 4 ga Afrilu, 2025.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Gusau.ya ce DSP Yazid Abubakar ne ya bayyana haka ga manema labarai a takardar da yasa mahannu ga manaima labarai a Gusau.
Acewar sa Tawagar kwararrun likitoci daga rundunar ‘yan sandan Najeriya sunyi gwaje-gwaje manyan cuturuka da sukafi addabar al’umma kamar,su HIV da Ciwon Anta(A, B, C) Hawan jini da gwajin matakin glucose, da dai sauran su.
A jawabin sa Kwamishinan CP Maikaba ya jaddada cewa shirin sadaukarwar ce da rundunar ta ke yi wajen bada taimako ga jama’a”.
“Bayan kare rayuka da dukiyoyin jama’a, mun himmatu wajen gudanar da ayyukan da za su inganta rayuwar al’umma kai tsaye, fitowar jama’a a yau yanuna cewa, rundunar ‘yan sanda tataka rawar gani wajan taimakon al’umma.
Yayin da ake ci gaba da gudanar da bukukuwan ranar ‘yan sanda ta kasa, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta sake jaddada aniyar ta na ganin ta hada aikin ‘yan sanda da ayyukan ci gaban al’umma.


